Wata Kungiyar masu kishin kasa ta bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu ya Sauke Shugaban hukumar aikawa da sakonni ta kasa NIPOST Tola Odeyemi, Saboda rashin sanin makamar aiki. Masu kishin kasan Sun bayyana hakan ne a Cikin wata Sanarwa da suka fitar a Abuja, Karkashin Jagorancin Kwamared AbdulWahab Tajuddeen, inda suka zargi Tola Odeyemi da karya ka’idojin aikin gwamnati. Acewar Masu korafin Shugaba hukumar tana barin kayayyakin jama’a na lalacewa a ofisoshin hukumar musamman a jihar Legas da kuma Abuja. Haka kuma, suna Zarginta da rashin zama a ofishinta inda…
Read MoreCategory: Siyasa
Siyasa
Majalisa Za Ta Dawo Da Sanata Ningi Bada Jimawa Ba – Shugaban Majalisar Dattawa
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce nan ba da dadewa ba majalisar za ta ?age dakatarwar da ta yi wa Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi ta Tsakiya). Hakan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan sanatan ya rubuta wasi?a ga Akpabio, inda ya yi barazanar daukar matakin shari’a idan ba a dage dakatarwar da aka yi masa ba cikin kwanaki 7. An dakatar da Ningi ne biyo bayan zargin da ya yi cewa an yi cushen N3.7m a kasafin kudin shekarar 2024, kamar yadda kafafen watsa labarai suka ruwaito. Bayan…
Read More‘Yan Adawa Ne Ke Zargin An Yi Cushe Cikin Kasafin Kudin 2024 – Tinubu
Shugaban ?asa Bola Tinubu ya bayyana cewa zargin da ake yi wai an dan?ara cushen ma?udan ku?a?e cikin kasafin 2024, kawai rashin fahimta ce da masu hauragiya ba su yi wa yadda ake lissafin ?idayar kasafin ku?i ba. Tinubu ya bayyana cewa masu adawa ba su iya bambance aringizo daban, lissafin-dokin-Rano ma daban. Da ya ke jawabi ranar Alhamis lokacin da ya gayyaci Sanatocin Najeriya yin bu?e-baki a Fadar Shugaban ?asa, Tinubu ya nuna goyon baya ga Sanatocin Najeriya, a inda ya yi magana a karon farko kan zargin maka…
Read MoreMatsalar Najeriya: Mun Gano Bakin Zaren – Gwamnatin Tarayya
Shugaba Bola Tinubu ya ce daga yanzu gwamnatin tarayya za ta samar da kayayyakin da aka kera a Najeriya a wani bangare na dabarunta na kara karfafa darajar Naira, inda ya bukaci ‘yan Najeriya su ma su yi hakan. Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a madadin shugaban sa yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnatin jihar kan shirye-shiryen da ake yi na karfafa naira. Ya ce gwamnati na mayar da hankali ne wajen tallafawa da…
Read MoreAn Zargi Shugabannin Majalisar Dattawa Da Rashin Adalci A Jagoranci
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban kwamitin da ke sa ido kan harkokin majalisar dattijan Najeriya ya yi korafi a kan yadda shugabannin majalisar ke nuna rashin adalci wajen jagoranci. Sanata Garba Musa Maidoki na PDP daga jihar Kebbi, ya shaida wa BBC cewa a yanzu ya lashi takobin fafutikar ganin an inganta yadda ayyukan Majalisar ke kasancewa domin ciyar da kasa gaba. Sanata mai doki ya ce lokaci da ya yi da wajibi a sanya bukatun al’umma kan gaba, maimakon yadda yawancin yan…
Read MoreBayyanar Peter Obi Wajen Tarsiri Ta Haifar Da Surutai
Rahotannin daga Suleja ta Jihar Neja na bayyana cewar a ranar Talata, 19 ga watan Maris aka gano tsohon gwamnan jihar Anambra a babban masallacin Suleja da ke kan hanyar Suleja zuwa Kaduna cikin jama’a yana sauraron tafsiri. An ganshi yana zaune a sahun gaba cikin daruruwan musulmi, yana sauraren tafsirin Al-Kur’ani da limamin masallacin yake gabatarwa. Wani ma’abocin dandalin X, @Imranmuhdz, ya wallafa bidiyon dan siyasar a lokacin da yake zaune a masallacin. Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan bidiyo na Peter Obi kamar haka: @OgaBossTweets…
Read MoreKungiyoyin Arewa Sun Yi Kiran A Janye Dakatarwar Da Aka Yi Wa Sanata Ningi
Gamayyar kungiyoyin Arewa ?arkashin wata kungiya mai suna RAID da aka kafa domin cigaban Arewacin Najeriya ta bukaci majalisar dattawa ta dawo da Abdul Ningi. Kungiyar RAID tana Allah wadai da yadda aka dakatar da Sanatan Bauchi ta tsakiya daga majalisa tare da yin tir da abin da ‘yan majalisar suka yi. Kungiyar tana ganin cewa an takawa ‘dan majalisar burki ne saboda ya yi namijin kokari wajen bankado irin rashin gaskiyar da ake tafkawa. RAID ta ce wannan mataki da aka dauka ya jawo an toshe bakin daya daga…
Read MoreCushe A Kasafin Kudi: A Yi Gaggawar Binciken Zargin Sanata Ningi – Atiku Abubakar
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya ce akwai bukatar a gudanar da kwakkwaran bincike kan zargin cushe a kasafin kudin Najeriya na 2024. Atiku ya yi kiran ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya ce yin rufa-rufa kan lamarin da kuma dakatar da wanda ya kwarmata zancen ba mafita ba ne. A ‘yan kwanakin da suka gabata, Sanata Abdul Ningi da ke wakiltar mazabar tsakiyar yankin jihar Bauchi a Majalisar Dattawa, ya yi zargin cewa…
Read MoreCushe Cikin Kasafi Bai Saba Doka Ba – Ministan Kasafin Kudi
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ministan kasafin kudi Alhaji Atiku Abubakar Bagudu yace ko kadan cushen da akayi cikin kasafin kudin Shekarar 2024 bai sa?a doka ba wanda har za a ta tayar da jijiyar wuya akai. Ministan na martani ne biyo bayan zargin cushe a kasafin kudin Najeriya da Sanata Abdul Ningi ya yi, wanda hakan ya kai ga dakatar da shi a Majalisar na tsawon watanni uku. A hannu guda ?an takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata…
Read MoreSanatocin Arewa Sun Zabi ‘Yar’adua A Matsayin Sabon Shugaba
Kungiyar Sanatocin arewacin Najeriya ta nada Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua da ke wakiltar Katsina ta tsakiya a zauren majalisar dattawan kasar a matsayin sabon shugaban kungiyar. Yar’Adua, wanda dan jam’iyyar APC ne – ya zama sabon shugaban kungiyar kwanaki biyu bayan saukar Sanata Abdul Ahmed Ningi – wanda dan jam’iyyar hamayya ta PDP ne – daga shugabancin kungiyar bayan da majalisar ta dakatar da shi wata uku. Sanata Ningi, wanda ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya a majalisar dattawan kasar, ya zargi gwamnatin kasar da yin cushen naira tiriliyan 3.7 a…
Read MoreBauchi: Gwamna Bala Ya Yi Tir Da Dakatarwar Da Aka Yi Wa Sanata Ningi
Gwamnatin jihar Bauchi ta nuna goyon bayanta ga dakataccen Sanatan jihar, Abdul Ningi. Gwamna Bala Mohammed shi ya bayyana haka yayin taron majalisar zartarwa a ranar Laraba 13 ga watan Maris. “Jiya na ji bakin ciki bayan dakatar da daya daga Sanatoci masu kyau a Bauchi saboda ya tsaya a kan gaskiya.” “Ban san menene za mu yi ba amma za mu yi magana ta sirri domin neman mafita kan lamarin.” “Ina tare da shi a ko da yaushe wannan ita ce matsayarmu musamman idan abin da ya ke fada…
Read MoreNi Da APC Mutu Ka Raba – Sanata Yari
Sanata Abdulaziz Yari daga Zamfara ta Yamma ya karyata rahoton da ke yawo na cewa ya hada kai da Atiku Abubakar domin kafa sabuwar jam’iyyar siyasa. Rahotannin sun ce ya hada kai da Abubakar, da kuma Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi da aka dakatar a halin yanzu don kafa jam’iyyar. An ruwaito cewa Atiku yana so ya kafa sabuwar jam’iyyar a matsayin wani shiri na kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027.S Sai dai Atiku ya musanta wannan zargin, inda ya bayyana cewa ya mayar da…
Read MoreTinubu Ya Bada Umarnin Bude Iyakokin Najeriya
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin sake bu?e kan iyakokin ?asar – ta sama da ta ?asa – da jamhuriyar Nijar. Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ?asar, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce shugaban ya bu?aci a bu?e iyakokin nan take ba tare da ?ata lokaci ba. Sanarwar ta ?ara da cewa shugaba Tinubu ya ?auki matakin ne sakamakon taron ?oli na kungiyar ECOWAS da aka gudanar a ranar 24 ga Fabrairu, 2024, a Abuja, inda shugabannin suka amince da ?age takunkuman tattalin arziki da aka kakaba…
Read MoreSanatocin Kudanci Sun Sabunta Kungiyar Su
Kwana guda bayan zazzafar muhawara a majalisar dattawa da ta haddasa dakatar da sanata Abdul Ningi, wanda shi ne shugaban ?ungiyar sanatocin arewacin Najeriya – sanatocin kudancin kasar sun farfa?o da ?ungiyarsu tare da za?ar shugabanni. ?ungiyar sanatocin kudancin ?asar ta za?i sanata, Adetokunbo Abiru mai wakiltar Legas ta gabas a matsayin sabon shugaban ?ungiyar. A baya dai shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan ?asar, Senator Opeyemi Bamidele ne ke jagorantar ?ungiyar. Sanatoci 51 ne daga jihohin kudancin ?asar 17 suka taro domin farfado da ?ungiyar, wata tara bayan ?addamar…
Read MoreIna Nan Daram A Jam’iyyar PDP – Atiku Abubakar
Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, Atiku Abubakar, ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da rahoton da ke cewa ya fice daga jam’iyyar. Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi alkawarin ci gaba da marawa jam’iyyar ta PDP baya yayin da yake bayar da shawarar a gaggauta hadewar jam’iyyun adawa. A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, ya ce “Na sha kiraye-kirayen ‘yan jam’iyyarmu da magoya bayanmu, da kuma ‘yan Najeriya da suka damu, dangane da labarin da aka buga da…
Read MoreNeman Mafita: Tinubu Ya Gana Da Tsohon Shugaban Kasa Babangida
Shugaba Bola Tinubu, ya ziyarci tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), inda suka yi wata ganawar sirri a gidansa da ke Jihar Neja. Tinubu ya zarce gidan tsohon shugaban kasar bayan halartar taron kaddamar da shirin manoma da Gwamna Mohammed Umaru Bago ya aiwatar a Minna, babban birnin Jihar Neja. Tinubu ya ziyarci Jihar Neja a ranar Litinin domin ziyarar aiki ta kwana daya domin kaddamar da gyaran tashar jirgin saman Minna wanda yanzu aka sauya masa suna zuwa Bola Ahmed Tinubu, da sauran…
Read More‘Yan Najeriya Za Su Yi Nadamar Rashin Zaman Mahaifina Minista – Bello El-Rufa’i
Dan Majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai ya ce Najeriya ta rasa jigo bayan majalisa ta ki amincewa da mahaifinsa. El-rufai ya ce kin amincewa da Majalisar ta yi da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai babbar asara ce ga kasar. Bello ya bayyana haka ne yayin hira da dan jarida Seun Okinbaloye da Punch ta ruwaito inda ya ce mahaifin nasa tun farko ba ya son mukamin. Ya ce sai da suka hadu da shi da sauran iyalansu domin rokon tsohon gwamnan ya karbi mukamin minista a gwamnatin…
Read MoreBadakalar Tiriliyan Hudu: Sanatocin Arewa Sun Koka Bisa Zargin Da Ake Wa Shugaban Majalisa
Sanatocin Arewa sun bayyana damuwarsu game da badakalar kasafin kudin da ake zargin Akpabio Kimanin Tiriliyan hu?u. Sanatoci daga yankin Arewa na kara nuna damuwarsu kan yadda Akpabio da mukarrabansa suka sanya ayyukan inganta kansu da suka kai Naira tiriliyan hudu a cikin kasafin kudin ta hanyar da bata dace ba. Mambobin kungiyar mai wakilai 58 ?ar?ashin jagorancin Abdul Ningi (PDP, Bauchi) sun tattauna a Ranar Alhamis a Gidan baki da ke gundumar Maitama a Abuja. A yayin hirarsa da Sashen Hausa na BBC, Abdul Ningi ya tabbatar da cewa…
Read MoreTinubu Ya Yi Gabas Mulkin Najeriya Ya Yi Yamma – Sanata Ningi
Shugaban ?ungiyar Sanatocin Arewacin kasa, Kuma Sanata daga Jihar Bauchi, Sanata Abdul Ahmed Ningi wanda ?an jam’iyyar hammaya ta PDP ne, ya ce abubuwan da shugaba Tinubu ya samu a ?asa sun tabarbare saboda irin wahalhalun da jama’a ke ciki. A hirar sa da Buhari Muh’d Fage,Ya ce: ”Bola Tinubu bai fahimci wannan kasar sosai ba, kuma bai fahimci wahalar mulki na kasa irin Najeriyar nan ba. Ba na ganin laifin sa da yawa saboda lokacin da yake neman shugabanci, ba wani alkawari da ya yi tsakanin sa da mutane,…
Read MoreTsaro: Gwamnatin APC Ta Gaza – Atiku
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, yayi tir da tabarbarewar harkokin tsaro a Kasar, Inda ya zargi Gwamnatin APC) da Gazawa wajen magance matsalar dake kara ta’azzara. Da yake kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen Ganin an kare ‘yan kasa da basu ji ba basu Gani ba Daga Masu Garkuwa Da Mutane Atiku ?an Takarar Shugaban ?asa a jam’iyyar PDP a Za?en 2023, ya nuna damuwarsa kan yadda Rashin tsaro da ya Addabi al’ummar ?asar Rahotannin baya-bayan nan da KBC Hausa ta fitar sun bayyana yadda wasu…
Read More