Shirin Labarina: Gaskiyar Abin Da Ya Faru Tsakanina Da Tashar Arewa 24 – Saira

Tun bayan da aka kammala nuna zango ba biyu na fim ?in Labarina mai dogon zongo, na kuma yi rubuta a shafina na Facebook cewa za mu sanar da lokacin da za a ci gaba da nuna zango na uku da kuma tashar da za a nuna, mutane da dama ke yin sharhi a kan lamarin daidai gwargwadon fahimtarsu.

Sai dai abin da ya fi shahara a bakunan mutane har ma da wasu kafofin watsa labarai shi ne kamfanin Saira Movies ya samu matsala da gidan talabijin din Arewa24 masu nuna Labarina, wasu ma har cewa suke yi ba za a ?ara nuna fim ?in a tashar ta Arewa24 ba.

Tun daga lokacin muke samun tambayoyi da dama ni da abokan aikina a Saira Movies kan gaskiyar lamarin da kuma jita-jitar da ake ya?awa.

Kuma hatta wasu ma’aikatan tashar Arewa24 sun tambaye ni wai me ke faruwa ne?

Ta wata fuskar lamarin ya kan ba ni mamaki, musamman ganin yadda jama’a suke kitsa labarin ?ala-?ato su ringa ya?a shi bayan sun san ?arya suke yi.

A wasu lokutan kuma ba na mamaki, domin hakan na nuna irin kar?uwar da shirin na Labarina ya samu a wajen masu kallo da kuma irin zumu?in da suke yi na ganin ci gabansa.

To amma a wani lokacin na kan yi takaici ganin cewa wasu kafofin watsa labarai na shiga cikin wannan yuyumar ta ya?a labaran ?anzon kurege, su ya?a abinda ba su da tabbas a kai, kawai don sun ga mutane na magana a kai. Tabbas irin wa?annan sun ci amanar aikin jarida.

Gaskiyar Lamari na yanke hukuncin yin wannan rubutu ne a BBC bayan tashar ta tuntu?e ni don jin ha?i?anin abinda ke faruwa da kuma jin gaskiyar lamari, tamkar dai sunan wani shiri na tashar ta BBC Daga Bakin Mai Ita.

Zance na gaskiya shi ne, mun shiga yarjejeniya da tashar Arewa24 don nuna fim ?in na Labarina mai dogon zango wanda kamfanin Saira moveis ne yake da ha??in mallakarsa.

Kamar yadda ake irin wannan yarjrjeniya a ko ina a duniya, mun amince cewa ba za mu bai wa kowa fim ?in zango na ?aya da na biyu ba tsawon shekaru biyu, ita kuma tashar ta Arewa24 za ta ringa nuna shi ne a talabijin da kuma sanya shi a manhajar Arewa24 on Demand.

Idan mu da Arewa24 muna bu?atar sabunta yarjejeniyar bayan shekara biyu za mu iya sake ?ulla wata, idan kuma ba ma bukata to shi kenan, magana ta kare.

A yanzu haka dai ba a na?i zango na uku da na hu?u na fim ?in Labarina ba, don haka babu wata yarjrjeniya tsakaninmu da kowa kan sabbin zangon da za a ?auka.

Kuma ko da ita tashar ta Arewa24 ba mu da wata yarjejeniya ko wata magana kan fim din, tun da ba za a yi maganar abin da babu shi a ?asa ba.

Ba za mu yi maganar inda za a nuna ci gaban shirin ba har sai mun kammala ?aukarsa, muka kuma kammala aiki a kansa.

A lokacin ne za mu iya shiga yarjejeniya da duk wa?anda suka ga ya burge su kuma ya kai irin mizanin da suka ajiye kafin su nuna wani shiri a kafarsu.

Sannan idan mun yi magana da su muka fahimci juna, sai mu sanar da jama’a cewa ga inda za a kalli sabon shirin.

Amma hakan ba ya nuna cewa mun samu wata matsala da tashar Arewa24 ko kuma ba za a ?ara nuna fin ?in a tashar ba.

A iya sanina a matsayina na mai shiryawa da ba da umarnin shirin ban san muna da wani sa?ani da Arewa24 ba, ko kuma rashin jin da?in mu’amalar da muka yi a baya ba.

Zan iya bugar kirji in ce dukkanmu mun ji da?in mu’amala da juna kuma ma zan iya cewa babu abinda zai hana mu sake kulla ala?a nan gaba idan dukkanmu mun amince da shara?an da za mu gabatawa juna.

Yaushe za a fara nuna ci gaban shirin Labarina?

Kawo yanzu dai ba mu sa rana ko lokacin da za a fara nuna ci gaban Labarina ba, domin kuwa har yanzu ba mu fara na?arsa ba.

Amma dai nan da makwanni biyu masu zuwa muke sa ran fara na?ar sabon shirin, kuma sai mun yi wata guda muna na?arsa sannan za mu iya samun haske kan yaushe za mu iya samar da fim ?in na adadin makwannin da za mu iya fara nunawa.

Amma dai duk da haka muna tabbatarwa da masu kallo cewa za ku ji da?in sabon shirin na Labarina, musamman ganin irin kar?uwar da ya samu a wajenku, kuma muna tabbatar muku cewa za mu yi kokari mu fara kawo muku shi ba tare da ?aukar dogon lokaci ba.

Aminu Saira shine Daraktan shirin LABARINA

BBC Landan

Related posts

Leave a Comment