Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin sake bu?e kan iyakokin ?asar – ta sama da ta ?asa – da jamhuriyar Nijar.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ?asar, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce shugaban ya bu?aci a bu?e iyakokin nan take ba tare da ?ata lokaci ba.
Sanarwar ta ?ara da cewa shugaba Tinubu ya ?auki matakin ne sakamakon taron ?oli na kungiyar ECOWAS da aka gudanar a ranar 24 ga Fabrairu, 2024, a Abuja, inda shugabannin suka amince da ?age takunkuman tattalin arziki da aka kakaba wa wasu ?asashen ?ungiyar, ciki har da jamhuriyar Nijar.
Ana sa ran ?age takunkumin zai rage zaman ?ar-dar da bun?asa harkokin kasuwanci da tattalin arziki tsakanin Najeriya da ?asashen da ke makwabtaka da ita.
Umurnin da shugaba Tinubu ya bayar ya kunshi matakai daban-daban da nufin maido da alakar da ke tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Daga cikin takunkuman da aka ?age sun hada da “Bu?e iyakokin ?asa da na sama tsakanin ?asashen biyu, da kuma na hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci da ke shiga da kuma fita daga Nijar.”
Haka kuma Najeriya ta sanar da ?age takunkumin hana bai wa Jamhuriyar Nijar wutar lantarki da a baya ta yi.
