Bauchi: Gwamna Bala Ya Yi Tir Da Dakatarwar Da Aka Yi Wa Sanata Ningi

IMG 20240314 WA0085(1)

Gwamnatin jihar Bauchi ta nuna goyon bayanta ga dakataccen Sanatan jihar, Abdul Ningi. Gwamna Bala Mohammed shi ya bayyana haka yayin taron majalisar zartarwa a ranar Laraba 13 ga watan Maris.

“Jiya na ji bakin ciki bayan dakatar da daya daga Sanatoci masu kyau a Bauchi saboda ya tsaya a kan gaskiya.”

“Ban san menene za mu yi ba amma za mu yi magana ta sirri domin neman mafita kan lamarin.” “Ina tare da shi a ko da yaushe wannan ita ce matsayarmu musamman idan abin da ya ke fada gaskiya ne.”

Wannan martanin na zuwa ne bayan dakatar da Sanata Abdul Ningi kan zargin da ya yi na cushe a kasafin kudin shekarar 2024.

Bayan cece-kuce a Majalisar kan zargin da sanatan ya yi, daga bisani Sanatoci da dama a Majalisar sun goyi bayan dakatar da shi har na tsawon watanni.

An dakatar da Ningi wanda ke wakiltar Bauchi ta tsakiya na tsawon watanni uku bayan wata doguwar mahawarar da aka yi a zauren Majalisar. Wannan na zuwa ne bayan Ningi ya yi zargin cewa cushen da aka yi a kasafin kudin zai illata kasar Najeriya baki daya.

 

Related posts

Leave a Comment