Ina Nan Daram A Jam’iyyar PDP – Atiku Abubakar

IMG 20240224 WA0211
Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, Atiku Abubakar, ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da rahoton da ke cewa ya fice daga jam’iyyar.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi alkawarin ci gaba da marawa jam’iyyar ta PDP baya yayin da yake bayar da shawarar a gaggauta hadewar jam’iyyun adawa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, ya ce “Na sha kiraye-kirayen ‘yan jam’iyyarmu da magoya bayanmu, da kuma ‘yan Najeriya da suka damu, dangane da labarin da aka buga da ke nuna ficewata daga jam’iyyar PDP.”

“Wannan tsantsar karya ce. Ina kara jaddada biyayyata ga jam’iyyar PDP yayin da nake ba da shawarar a gaggauta hadewar jam’iyyun adawa.” In ji Atiku Abubakar.

Related posts

Leave a Comment