Shugaban ?asa Bola Tinubu ya bayyana cewa zargin da ake yi wai an dan?ara cushen ma?udan ku?a?e cikin kasafin 2024, kawai rashin fahimta ce da masu hauragiya ba su yi wa yadda ake lissafin ?idayar kasafin ku?i ba.
Tinubu ya bayyana cewa masu adawa ba su iya bambance aringizo daban, lissafin-dokin-Rano ma daban.
Da ya ke jawabi ranar Alhamis lokacin da ya gayyaci Sanatocin Najeriya yin bu?e-baki a Fadar Shugaban ?asa, Tinubu ya nuna goyon baya ga Sanatocin Najeriya, a inda ya yi magana a karon farko kan zargin maka ma?udan a?aluman ku?a?e a cikin kasafin, lamarin da ya haifar da ka-ce-na-ce.
Tinubu ya ce shi dai ya fahimci asar?alar da ke tattare da lissafin al?aluman kasafin ku?i, wadda sai mai kaifin fahimta ke iya ganewa. Ya ce amma masu adawa idon su ya rufe ba za su iya fahimta ba.
Daga nan ya yi wa Sanatocin addu’a fatan alheri dangane da yadda suka daddale kasafin ku?i na 2024.
“Ni dai na san yadda lissafin al?aluman kasafin ku?i yake. Kuma adadin da na kai Majalisar Dattawa na sani sarai. Na san kuma adadin da aka maido min.
“Saboda haka ina gode maku baki ?aya saboda yadda kuka bibiyi kasafin tare da daddale shi. Na gode ?warai.
“Wa?anda ke surutan wai an kafci ma?udan ku?a?e an cusa a cikin kasafin da gangan, ai ba su san bambancin aringizo da lissafin-dokin-Rano a ?ididdiga ba. Kuma ba su koma sun nazarci ainihin adadin da na aika Majalisa ba. Saboda haka ba ku aikata wata har?alla ko aringizo komai ba,” inji Tinubu.
