Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa jigon Jam’iyyar NNPP Mai kayan Marmari, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya ziyarci tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El’rufai a gidan sa dake babban Birnin tarayya Abuja. Ana dai ganin ziyarar na da ala?a da El-Rufai na shirin barin APC zuwa NNPC dan takawa Tinubu Birke da kuma marama Rabiu Musa Kwankwaso baya dan za?en 2027 kamar yadda masu sharhi suka bayyana. Akwai tsohuwar alaka tsakanin Kwankwaso da El’rufai tun lokacin yana Ministan tsaro shi Kuma yayi Ministan Birnin…
Read MoreCategory: Siyasa
Siyasa
Zuwa Kotu: El-Rufa’i Ya Yi Riga Malam Masallaci – Majalisa
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi watsi da karar da tsohon gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai ya shigar gaban wata kotun tarayya inda yake kalubalantar rahoton Majalisar da ya zarge shi da almundahana da ku?in gwamnati a lokacin mulkinsa. Shi dai tsohon gwamnan na zargin Majalisar ne da take masa hakki kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar. Ita dai Majalisar dokokin jihar Kaduna a martanin da ta mayar, ta ce ta yi matukar mamaki ne yadda tsohon gwamnan ya ruga zuwa kotu, yana kalubalantar sakamakon binciken da kwamitinta…
Read MoreKADUNA: Zan Dawo Da Martabar PDP Idan Na Zama Shugaban Jam’iyya – Edward Auta
Dan takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP na jihar Kaduna Edward Pama Auta, ya bayyana aniyarsa na dawo da martabar Jam’iyyar da ha?a kan daukacin ‘ya’yan jam’iyyar a matakai daban-daban idan ya samu nasarar lashe za?en Shugabancin Jam’iyyar wanda za’a gudanar nan gaba kadan. Edward Pama Auta, ya bayyana haka ne yayin da ya kaiwa tsohon Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Kuma tsohon Gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Mohammed Ma?arfi a gidansa dake Kaduna domin neman goyon bayansu inda yayi Alkawarin Farfado Da martabar Jam’iyyar. Auta, ya tabbatarwa tsohon Shugaban cewa idan…
Read MoreZamfara: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ana Sallar Asubah
‘Yan bindiga sun kai hari Masallaci a lokacin da mutane ke shirin Sallar Asuba a kauyen Tazame da ke ?aramar hukumar Bungudu a Zamfara Rahotanni sun nuna cewa ?an bindigar sun kashe ladan da ?aninsa, sun yi awon gaba da mutane da dama ran Talata da safe Kakakin rundunar ?an sandan jihar, ASP Yazid Abubakar ya ce sun tura karin jami’ai zuws garin domin dawo zaman lafiya Wani mazaunin kauyen ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun far wa mazaunar kauyen ne a lokacin Sallar Asuba.…
Read MoreAn Gabatar Da Kudirin Dokar Yin Gyara Ga Masarautar Sarkin Musulmi
An gabatar da kudirin dokar yin gyara ga sashe na 76, kashi na biyu na dokar ?ananan hukumomin jihar Sokoto a gaban majalisar dokokin jihar a jiya Talata. ?udurin dai ya janyo ce-ce-kui-ce, kasancewar ana ganin idan aka amince da dokar za ta rage ?arfin iko na mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Sa’ad Abubakar III. Bayan gabatar da ?udurin a zauren majalisar, nan take aka yi masa karatu na farko da na biyu, sannan aka mi?a shi ga kwamitin da ke lura da ?ananan hukumomi da masarautu. An bai wa…
Read MoreDalilina Na Ziyartar Tsohon Shugaban Kasa Buhari – Atiku
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon shugaban ?asar, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina. ?an takarar shugaban ?asa a za?en 2023 a ?ar?ashin jam’iyyar PDP ya kai ziyarar ne tare da rakiyar wasu manyan abokan siyasarsa. A sa?on da Atiku Abubkar ya wallafa a shafinsa na X, tsohon mataimakin shugaban ?asar ya ce ya kai wa tsohon shugaban Najeriyar ziyara ne domin yin ”gaisuwar Sallah” Ziyarar ta Atiku Abubakar ta zo ne kwana uku bayan ya ziyarci tsaffin shugabannin Najeriya, Ibrahim Babangida da…
Read MoreDambarwar Sarautar Kano: Gwamnatin Kano Ta Zargi ‘Yan Sanda Da Nuna Bangaranci
Gwamnatin jihar Kano ta zargi ?an sanda a jihar da nuna ?angaranci a dambarwar masarautar da taki ci taki cinyewa a jihar. Mai magana da yawun gwamnan jihar Mal Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan yayin wata hira da tashar Talabijin ta Channels a ranar Juma’a. Dawakin Tofa ya bayyana muhimmancin dawo da martabar sarautar kano da ya zargi tsohuwar Gwamnatin Ganduje da rusawa. A hannu guda kuma gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya zargi gwamnatin da ta gabace shi da ?aukar nauyin ‘yan daba a Kano.…
Read MoreKaduna: Gabar Siyasa Na Kara Kamari A Tsakanin El-Rufai Da Uba Sani
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmed El-Rufai, ya ce bai damu da yun?urin da majalisar dokokin jihar ke yi na bincikar gwamnatinsa ba. El-Rufai ya yi nuni da cewa mai yiwuwa gwamnatin ba za ta yi nasara ba. Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana hakan a wani taron Sallah da ya yi da mu?arrabansa a ranar Talata 18 ga watan Yunin 2024. El-Rufai ya kuma shawarce su da su guji yin cacar baki da hadiman gwamnan, inda ya yi hasashen…
Read MoreBabu Wanda Ya Isa Ya Yi Mana Barazana Kan Rikicin Sarautar Kano – Kwankwaso
?an takarar shugaban kasan Jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi Gwamnatin Tarayya da biye shawarar wasu makiyan Kano don wargaza zaman lafiya da aka san jihar. Da yake tsokaci kan rikicin Sarautar Kano, Kwankwaso ya zargi hukumomin tsaron Gwamnatin Tarayya da goyon baya Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, sabanin aikinsu na tabbatar da tsaro da kuma doka da oda a jihar. A cewarsa, “Muna da dimbin mabiya saboda jama’a sun amince da mu kasancewar muna tare da su, kuma a shirye gwamnain NNPP…
Read MoreKu Kara Hakuri Ina Sane Da Halin Kuncin Da Ku Ke Ciki – Tinubu Ga ‘Yan Najeriya
A sakon sa na bikin ranar dimokiradiya ta bana, wadda ke nuna yadda aka kwashe shekaru 25 ana gudanar da ita ba tare da samun targade ba. Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ‘yan Najeriya hakuri game da halin matsin da suka samu kan su, wanda yace yana sane da shi, kuma nan gaba kadan za su dara. Shugaban ya kuma bayyana shirin gabatar da kudirin yiwa sabuwar dokar albashi gyaran fuska domin amincewa da sabon karin da ake tattaunawa a kai. A yayin da ya ke jawabin,…
Read MoreYobe: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Dukkanin Kananan Hukumomin Jihar
Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 17 da aka kammala zaben kananan hukumomin jihar. Haka kuma jam’iyyar ta lashe dukkan kujerun kansiloli 178 na jihar. Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Yobe, YOSIEC, Dr Mamman Muhammad, ne ya bayyana hakan a hedikwatar hukumar da ke Damaturu a ranar Lahadi. “APC ta lashe dukkan kujeru 17 da kansiloli 178 a zaben kananan hukumomin jihar,” in ji shi. Ya kara da cewa hukumar ta karba, ta duba, ta tantance tare da amincewa da sakamakon kowanne…
Read More12 Ga Watan Yuni: Bama Goyon Bayan Duk Wata Zanga-Zanga – Kungiyar Matasan Arewa
Kungiyar cigaban Matasan Arewa (AYCF) ta bayyana damuwa kan wasu rahotanni dake bayyana cewar wasu gungun jama’a na shirin gudanar da zanga-zanga domin haifar da rudani a bikin ranar dumukaradiyya ta 12 ga watan Yuni dake tafe. A cikin wata takardar sanarwa da shugaban kungiyar ta matasan na Arewa Yerima Shettima ya fitar kuma aka rarraba wa manema labarai a Kaduna, ya yi tir gami da Allah wadai da duk wani shirin zanga-zanga da wasu za suyi musamman a ranar bikin 12 ga watan Yuni, wanda Najeriya ke murnar ranar…
Read MoreAn Sha Yi Mini Barazanar Kisa, Sakamakon Sukar El-Rufai – Shehu Sani
Tsohon Sanatan Jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani kuma ?an gwagwarmayar kwatar yanci ya bayyana cewa, sau ba adadi an yi masa barazanar kisa kawai don ya bayyana cewa, gwamnatin Malam Nasiru El-Rufai tafi ko wace gwamnati sata a tarihin Jihar Kaduna.. Shehu Sani ya bayyana haka ne yayin wata hira da a ka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV a daren ranar Juma’a.. Haka zalika Sanata Shehu sani yayi rubuce-rubuce da dama akan irin satar da gwamnatin jihar Kaduna keyi a lokacin mulkin Malam Nasiru El-Rufai, a…
Read MoreMuna Kokarin Saisaita Rayuwar Matsi Da ‘Yan Najeriya Ke Ciki – Tinubu
Sugaban kasa Bola Tinubu ya sake jaddada cewa yana sane da halin matsin rayuwa da ‘yan ?asar ke fama da shi. Yayin da yake jawabi a wajen bikin ?addamar da aikin titin Guzape Lot II, a Abuja babban birnin ?asar ranar Asabar, shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya dace domin sau?a?a wa ‘yan ?asar halin matsin rayuwar da suke fuskanta. “Wannan lokaci ne mawuyaci a ?asarmu,Har yanzu muna ?o?arin saisaita tsarin tattalin arzikin ?asar, domin kawo sau?i da ingantuwar tattalin arzikin ?asarmu,” in ji…
Read MoreKaduna: Ba Mu Yi Mamakin Binciken El-Rufai Ba – PDP
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da tafka muhawara kan zargin tafka almundahana da Majalisar dokokin jihar ta yi wa tsohon gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai a shekaru takwas da ya yi a kan mulki. Jamiyyar adawa ta PDP a jihar ta ce ta san za’a rina, kuma za ta zura ido ta ga irin matakan da gwamnatin APC a jihar za ta dauka. Dan takarar gwamna a jam’iyar PDP a Kadunan a zaben 2023, Hon Isa Asiru Kudan, ya shaida…
Read MoreSaukar Da Farashin Kayayyaki ‘Yan Najeriya Ke Bukata Ba ?arancin Albashi Ba – PDP
Wani Jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Delta Sunny Onuesoke ya ce, ?arin mafi karancin albashi ba shine maganin matsalar tsadar rayuwa da ake fuskanta ba, illa saukar da farashin kayayyakin abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum. Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a wani martanin da ya mayar dangane da yadda take kasancewa tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago a kasar nan. Onuesoke ya ce ?arin albashin ba zai magance matsalar tattalin arzikin kasar ba face ma ya ?ara dagula al’amurra.…
Read MoreDambarwar Masarautar Kano: Kotu Ta Dage Zama Zuwa 13 Ga Watan Yuni
Rahotannin dake shigo mana daga birnin Kano na bayyana cewa a daidai ?arfe 2:35 na rana Alhamis ne Mai Shari’a a Babbar Kotun Tarayya da ke Gya?i-gya?i, kan titin ‘Court Road’ ta ?age sauraren ?arar da dambawar masarautar Kano, zuwa ranar 13 ga Yuni. Kotun ta ce a koma ranar 13 ga Yuni domin ta tabbatar shin ta na da hurumin sauraren ?arar da tsigaggen Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba ?an’Agundi ya shigar, wadda ya ?alubalanci rushe masarautar Kano, lamarin da ya shafi har da rawanin sa. Gidan Radiyon Dala…
Read MoreJuyin Mulki Ba Ya Faruwa Sai Da Sa Hannun ‘Yan Siyasa – Abdulsalami Abubakar
Tsohon Shugaban ?asa Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa juyin mulkin soja ba zai iya faruwa ba sai da hannun ‘yan siyasa. Abdulsalami, shugaban mulkin soja na karshe a Najeriya, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar Sun. KBC News ta ruwaito cewa an yi juyin mulki da dama a yammacin Afirka kwanan nan. A bara ne dai sojoji suka hambarar da zababben shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum bisa tafarkin dimokuradiyya. Abdulsalami ya shiga tsakani ne a madadin kungiyar ECOWAS ta yankin, bayan da aka kakabawa…
Read MoreEFCC Ba Ta Binciki Kwankwaso Ba – Shugaban Jam’iyyar NNPP
Shugaban jam’iyyar, NNPP, a jihar Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa ya ce masu zagon kasa ba za su iya dakatar da makomar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, Rabiu Kwankwaso ba. Dungurawa ya ce wadanda ke yakar Kwankwaso ne bayan rahotannin da ke cewa Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC na binciken sa. Rahotanni sun bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa na binciken Kwankwaso kan badakalar Naira biliyan 2.5. Sai dai da yake jawabi ga manema labarai a Kano, jigon na…
Read MorePeter Obi Ya Ziyarci Helkwatar Jam’iyyar Labour Da Amincewa Da Sabbin ‘Yan Kwamitin Gudanarwa
?an takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi, ya bi sahun dandazon magoya bayan jam’iyyar, inda ya ziyarci shagabannin jam’iyyar a helkwatar su da ke Abuja. Shugaban jam’iyyar na kasa wanda ya kaddamar da sabbin ‘yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar a karkashin jagorancin Barista Julius Abure, ya bukaci ‘yan kwamitin su sanya rayuwar ‘yan Nijeriya da ma kasa baki daya a sahun farko na dukkan al’amurran su. Peter Obi, ya ce ya kasance a sakatariyar jam’iyyar ne musamman don ya ziyarci shugaban ta, ya na mai shan alwashin ci-gaba…
Read More