2023: Za Mu Cure Wuri Guda Domin Kwatar Mulki – ‘Yan Takarar PDP

Tsohon shugaban majalisan Dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa jam’iyyar PDP a shirye take ta amince da zabin ?an takaran shigaban kasa daya idan hakan ya zama dole a tsakanin su.

Saraki ya bayyana haka a garin Bauchi a lokacin da ya kai ziyara ga gwamnan Bauchi tare da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

” Abinda ya kawo mu garin Bauchi shine don mu gana a tsakanin mu mu ga yadda za a yi a samu daidaituwa a tsakanin mu domin samun matsaya ?aya idan hakan ya taso.

” Dukkan mu uku da muka bayyana ra’ayin mu na takarar shugabancin kasar nan, za mu iya dukkan mu. Amma kuma dole mu saka kasar mu a gaba kafin burin mu ya biyo baya.

” Za mu ci gaba da tattaunawa a tsakanin mu domin samun matsaya ?aya sannan kuma za mu ci gaba da yin haka har sai mun cimma matsaya a tsakanin mu tukunna domin Jam’iyyar mu da kasar mu baki ?aya.

Related posts

Leave a Comment