Tsohon shugaban majalisan Dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa jamiyyar PDP a shirye take ta amince da zabin ?an takaran shigaban kasa daya idan hakan ya zama dole a tsakanin su.
Saraki ya bayyana haka a garin Bauchi a lokacin da ya kai ziyara ga gwamnan Bauchi tare da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.
Abinda ya kawo mu garin Bauchi shine don mu gana a tsakanin mu mu ga yadda za a yi a samu daidaituwa a tsakanin mu domin samun matsaya ?aya idan hakan ya taso.
Dukkan mu uku da muka bayyana raayin mu na takarar shugabancin kasar nan, za mu iya dukkan mu. Amma kuma dole mu saka kasar mu a gaba kafin burin mu ya biyo baya.
Za mu ci gaba da tattaunawa a tsakanin mu domin samun matsaya ?aya sannan kuma za mu ci gaba da yin haka har sai mun cimma matsaya a tsakanin mu tukunna domin Jamiyyar mu da kasar mu baki ?aya.

