?an takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar PDP Isah Ashiru Kudan, ya yi kira ga gwamnan Nasir El-Rufa’i ya dakatar da korar ma’aikatan da ya ke yi a jihar ba tare da bata lokaci ba.
Idan dai ba a manta ba, gwamnatin El-Rufai ta kori malaman makarantun firamare, ciki har da shugaban kungiyar malamai ta kasa wanda ?an asalin jihar Kaduna ne.
Isah Ashiru ya soki hakan ne a cikin wani sako da ya fitar, inda ya ce a wannan lokaci da talaka ke hannu-baka-hannu- kwarya bai kamata a ce an gallaza ma shi da irin wannan azaba ta korar aiki da rana tsaka ba.
Ya ce ana fama da talauci da wahalhalun rayuwa sai kuma a wayi gari ?an aikin da talaka ke samun abinci an kore shi, wannan rashin imani ne.
A karshe ya yi kira ga gwamna El-Rufa’i ya dakatar da korar ma’aikatan da ya ke yi, domin a halin yanzu al’ummar jihar Kaduna su na fuskantar matsalolin rayuwa daban-daban, don haka idan ba a tallafa masu ba to bai kamata a ce ana raba su da ayyukan da su ka dogara da su domin ciyar da iyalan su
ba.
