Rashin Iya Jagorancin Buhari Ne Silar Matsalolin Najeriya – Mr LA

An bayyana damuwa da takaici dangane da halin rayuwar kunci da talakawan kasar nan suka shiga sakamakon rashin Man fetur, iskar Gas, tsaro da kuma hasken wutar lantarki.

Hoborabul Lawal Adamu Usman wanda aka fi sani da suna Mr LA jigo a jam’iyyar PDP ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna.

“Duk duniya babu kasar da bata san adadin albarkatun man da take hakowa ba sai Najeriya kuma a Karkashin jagorancin Shugaban kasa wanda shine Ministan man fetur”.

“Sakaci da rashin iya jagorancin Shugaba Buhari ya sa matatun Man da muke da su ya kasa ri?e su balantana har mu sa ran samun sababbin da yayi alkawarin ginawa duk shekara”.

“Wannan dalilin ya sa duk da farashin gangar mai ya karu a kasuwar duniya yanzu zuwa dala 105-110 hakan bai yi tasiri a Najeriya ba, domin idan akwai Shugabanci nagari da lalubo hanyar kawowa talakawa sauki a rayuwar su, a yadda farashin man ya yi daraja a kasuwar duniya saukin sa ya kamata a samu ba wai rashin sa ba”.

Mr LA ya cigaba da cewar Man Dizel shine abin da kashi 70 na kamfanonin kasar nan ke anfani dashi na ayyukan su na yau da kullum, kuma da shi ne manyan motoci ke jigilar kayayyakin masarufi daga arewa zuwa kudancin kasar nan.

A halin yanzu farashin Dizel ya tashi daga 430 zuwa 700, ka ga dole kayayyakin amfani na yau da kullum su tashi sakamakon ku?in sufuri da ya tashi, man Dizel wanda a baya lokacin da matatun mai ke aiki bai wuce 180 ba duk lita ba amma yanzu ya zarce 700″

?an siyasar ya kuma yi tsokaci akan fannin wuta inda ya ce babu wani cigaba da aka samu tun bayan hawan shugaba Buhari kan mulki. Ya samu kasar da karfin wuta megawat 4500 wanda a maimakon ya karu kullum kara tabarbarewa abin ya keyi wanda hakan ba karamar illa bane ga tattalin arzikin kasar, muddin aka gyara wutar kasar nan matsaloli da dama zasu ragu.

Related posts

Leave a Comment