Hukumar DSS Ta Bankado Shirin Tayar Da Rikici A Najeriya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jami’an Tsaron Sirri na SSS sun bayyana cewa sun banka?o wani shirin tayar da tashin hankali a wasu yankunan Najeriya, musamman ma a Tsakiyar Najeriya.

SSS sun bayyana haka a cikin wata sanarwa da Kakakin Ya?a Labarai na rundunar, Peter Afunanya ya fitar a ranar Asabar. Sanarwar ta ce masu ?o?arin shirya tarzomar na son yin maye-fake-da-annoba, wato fakewa da matsalar wutar lantarki su tada tarzomar.

DSS sun fallasa tuggun a daidai lokacin da matsalar wutar lantarki da kuma matsalar fetur wadda ta yi ?amari tun a farkon Fabrairu.

An dai fara shiga matsalar ce a farkon sabuwar shekara, tun daga shigo da gur?ataccen fetur daga Belgium.

?arancin fetur ?in ya haifar da dogayen layukan sayen fetur a gidajen mai ?in fa?in ?asar nan, sannan kuma ya haifar da tsadar sa.

Lamari ba a fetur ka?ai ya tsaya ba, har da man dizal, wanda a yanzu litar sa ?aya ta kai naira 720.

A cikin sanarwar DSS, sun ce wa?anda ke son tayar da rikicin sun yi niyyar amfani da ?aliban jami’o’i da na sauran manyan makarantu da kuma malaman jami’o’i, wa?anda a yanzu ke zaune gida saboda yajin aikin da ASUU ke ci gaba da yi.

“?o?arin su shi ne haddasa rikicin addini da na ?abilanci, daga nan sai wa?anda aka ?warya kuma sai a zuga su domin su ?auki fansa, sai ?asa ta dagule, yadda batun siyasa zai ?ara zafi sosai.

“A ?o?arin cimma wannan mummunar manufa ta su, sun gudanar da taruka a ciki da wajen wuraren da su ke so su tayar da rigingimun.

“Kuma DSS na sane da ?o?arin da su ke yi ta hanyar yin amfani da ?alibai da malaman jami’o’i, ?ungiyoyin kishin jama’a, Kungiyoyin ?wadago da kuma tantagaryar ?atagari, domin shirya tarzoma makammanciyar irin ta #EndSARS.

DSS ta ce babu ruwan wa?annan mutane da duba ?o?arin da gwamanti ke yi domin kawo ?arshen matsalolin.”

Daga nan DSS ta ja hankalin masu wannan mummunan shiri cewa su shiga taitayin su.

Related posts

Leave a Comment