Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewa a daren ranar Litinin ne ?an ta’adda suka kashe wani babban kwamandan rundunar bijilante na jihar Zamfara (CPG), Aminu Sarkin-Baura, da wani jami’in rundunar da ba a bayyana sunansa ba, yayin da suke kokarin dakile wani harin da ‘yan ta’adda suka kai a garin Tsafe.
Mazauna yankin sun ce ?an ta’addan sun mamaye garin wanda hedikwatar karamar hukumar Tsafe ne da tsakar rana inda suka yi garkuwa da wasu ma’aikatan aikin gina titi guda 14 a gidansu da ke garin.
Sun ?ara da cewa Sarkin-Baura da tawagarsa sun hada kai da sojoji wajen yin arangama da ?an ta’addan a lokacin da suka kawo harin.
Mazauna yankin sun ce ?an ta’addan sun yikona motoci biyu na jami’an tsaron. Sannan kuma ko da suka shiga garin tsafe sun wuce ne kai tsaye zuwa gidan ma’aikatan da ke aikin titin Funtua-Gusau inda suka arce da ma’aikata 14.
