Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewa a daren ranar Litinin ne ?an taadda suka kashe wani babban kwamandan rundunar bijilante na jihar Zamfara (CPG), Aminu Sarkin-Baura, da wani jamiin rundunar da ba a bayyana sunansa ba, yayin da suke kokarin dakile wani harin da yan taadda suka kai a garin Tsafe.
Mazauna yankin sun ce ?an taaddan sun mamaye garin wanda hedikwatar karamar hukumar Tsafe ne da tsakar rana inda suka yi garkuwa da wasu maaikatan aikin gina titi guda 14 a gidansu da ke garin.
Sun ?ara da cewa Sarkin-Baura da tawagarsa sun hada kai da sojoji wajen yin arangama da ?an taaddan a lokacin da suka kawo harin.
Mazauna yankin sun ce ?an taaddan sun yikona motoci biyu na jamian tsaron. Sannan kuma ko da suka shiga garin tsafe sun wuce ne kai tsaye zuwa gidan maaikatan da ke aikin titin Funtua-Gusau inda suka arce da maaikata 14.

