Babban hafsan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ya ce masu ba da bayannan sirri ga sojojin ke kawo cikas ga yaki da kungiyoyin masu garkuwa da mutane da ke ci gaba da sace dalibai da mazauna arewacin kasar.
Janar Musa ya bayyana hakan ne a ranar Litinin.
A ranar Lahadin da ta gabata ne rundunar sojin ta sanar da kubutar da dalibai 137 da wasu ‘yan bindiga suka sace a farkon watan nan a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar. ‘Yan makarantar sun isa Kaduna ne a ranar Litinin.
Musa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sojoji a matse suke kuma galibi suna dogara ne ga masu ba da bayannan sirri don bin gungun masu dauke da makamai, wadanda aka fi sani da ‘yan bindiga a cikin gida, ba tare da samun nasara ba.
“Su masu ba da bayannan sirri su kan sa sojojin su je wani wuri na daban, sai sun isa wurin sai su tarar ba komai,” in ji Musa.
