Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar a zaman da majalisar dokokin Jihar ta yi a ranar Laraba, majalisar ta amince da tsige mataimakin gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau.
Kuma ba tare da bata lokaci ba Majalisar ta na?a Sanata Hassan Nasiha a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar ta Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewar tsohon mataimakin Gwamna Mahdi Gusau ya saka kafar wando ?aya da gwamnan jihar Alhaji Bello Matawalle tun bayan ?in sauya sheka zuwa jam’iyyar APC da yayi.
Majalisar jihar ta tuhume shi da wasu laifuka wanda Mahdi ya fito ya bayyana cewa ba zai bayyana a gabanta ba saboda maganar zargi da ake masa ya na gaban kotu.
Hakan bai hana majalisar tsige shi ba a ranar yau Laraba ba.
Kakakin majalisar Nasiru Magarya ya ce kwamitin da majalisar ta na?a ya tabbatar da laifukan da Mahdi ya aikata wanda a dalilin haka ya sa majalisar ta tsigeshi.
