Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta kai ziyarar ba-zata zaurukan Majalisar kasar guda biyu, wato ta Dattawa da ta Wakilai.
Ziyarar ta zo daidai da lokacin da majalisar ke gabatar da gyara-gyaren kundin tsarin mulkin kasar, inda zuwan nata ya nuna alamar goyon baya ga aikin da Majalisar ta yi musamman kan fannin da ya kebe wa mata kujera daya a kowace jiha tare da ta ‘Yan majalisar wakilai guda biyu.
Matan Najeriya sun dade suna fata da ?okin samun wannan dama na neman kari na mukaman siyasa da a yanzu kashi uku kacal suke da shi a majalisar dokokin kasar.
Da take zantawa da manema labarai jim ka?an bayan kammala ziyarar Aisha Buhari ta ce ta zo ne ta saurari bayanai da aka yi a kan gyaran Kundin tsarin mulkin Kasa, musamman ma bangaren da aka ware domin mata. Ta ce ta ji dadi kwarai da wannan nasara da aka samu.
