Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kafofin watsa labarai na zamani ya bayyana goyon bayansa ga Asiwaju Bola Tinubu, jigon jam’iyyar APC mai son darewa shugabancin kasa a 2023.
A ranar Laraba, Bashir Ahmad, daya daga cikin hadiman Buhari, ya shiga jerin masoya kuma magoya bayan Tinubu domin shugabancin kasa a shekarar za?e ta 2023.
Bashir Ahmad ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu a yayin martani ga tambayar da aka yi masa a Twitter. A yayin wallafa ta shafin @slywhite0012, wani Sylva White ya yi tambaya: “Bashir, ina son tambayar ka kuma ina son amsa ta gaskiya ba tare da son ka ba. Tsakanin Tinubu da Jonathan, wanne za ka fi so ya karba shugabancin daga ubangidanka? A yayin martani ga tambayar hadimin shugaban kasa ya ce: “Asiwaju Bola Ahmed Tinubu!”
