Saura ?iris A Gama Da Arewa – Sheikh Gadon ?aya

Shahararren malamin addinin musuluncin nan Sheikh Abdullahi Gadon Kaya ya bayyana cewar ana dab da cin arewacin kasar nan da ya?i muddin Shugabanni yankin basu dauki matakin da ya dace ba.


Malamin ya bayyana hakan ne a wata huduba da yayi a masallacin Khalid bn Walid dake bakin ruwa Kaduna.

‘ A halin da muke ciki a arewacin kasar nan an bar yaran mu kusan kimanin shekara daya a gida sakamakon yajin aikin da malaman jami’o’i suke yi saboda wasu dalilai da wasu marasa kishin kasar nan basa son a kawo karshen sa. Bukatun ASU a fili yake kuma babu inda su kace a kara masu kudin albashi, suna bukatar a inganta ilimin yaran talakawan kasar nan ne Amman wasu marasa kishi sunki bari ayi hakan saboda Suna da wata manufa. Inji Sheikh Abdullahi Gadon Kaya”

Malamin yace a arewacin kasar nan an bar matasan mu na ta’ammuli da miyagun kwayoyi kamar babu gwamnati. Matan aure na shan kwaya, matasan mu kwaya, yaran mu masu kananan shekaru na shan kwaya. Ta yaya za asamu manya nan gaba masu tunani?

Kuma hukumomin kasar nan sun san yadda ake shigo da kwayoyin nan amma haryanzu anki a kawo karshen sa. Idan har gwamnati zata iya kawo karshen shigo da shinkafa ta boda me zai hana a kawo karshen shigo da miyagun kwaya kasar nan?

A binciken da mu kayi ya nuna mana anfi ta’ammuli da siyan kayan maye a arewa fiye da kudancin kasar nan duk da mafi yawanci daga chan kudancin kasar nan ake sarrafo su.

Yaran nan masu garkuwa da mutane duk yaran mu ne, kuma muna kallo amman son zuciya ya hana kowa magana. Meyasa ba zamu taimakawa jami’an tsaron mu ba wurin kawo karshen matsalar tsaron da yake cin rayukan muatnen yankin mu a koda yaushe?

Wallahi inda a kudancin kasar nan ne ake garkuwa da mutane tare da kashe mutane babu gaira babu dalili da yanzu an kawo karshen matsalar. Ya zama wajibi Shuwagabannin mu su farka daga barcin da su keyi kamin matsalar ta gagari kowa.

Related posts

Leave a Comment