Ronald Koeman Zai Cigaba Da Horas Da Kungiyar Bercelona

Kocin dan kasar Netherlands wanda ke fuskantar kalubale a bana, ya ja ragamar wasa biyu a jere da aka doke Barcelona a Champions League, sannan kungiyar bata kokari a La Liga ta kakar nan.

Barcelona ta ziyarci Atletico Madrid a wasan hamayya karawar mako na takwas a gasar La Liga da za su kece raini ranar Asabar.

Laporta ya ce: “Koeman zai ci gaba da zama kocin Barca, koda wasan Atletico ya yi kyau ko akasin hakan.

Shugaban ya kara da cewar ”Mun fuskanci yana bukatar karin lokaci da hakuri: Kuma yana kaunar Barca, sannan tsohon zakakurin dan wasan kungiyar ne, zai ci gaba da jan ragamar kungiyar.

“Yana kuma kaunar kungiyar shi ya sa ya amince ya horar da Barca a lokacin da muke fuskantar kalubale.

“Bayan da na tattauna da shi na fahimci ya amince da ‘yan wasan da yake da su …. kuma ba gaskiya bane cewar ba jituwa tsakani na da shi – alaka ce mai kyau da aminci a tsakaninmu.”

Ranar Juma’a Koeman ya ce ya gaji da kare kansa, kan sakamakon wasanni ”Ba wanda ya ce min komai dangane da makoma ta a Barcelona”.

Sai dai tsohon kocin Everton bai ce komai ba kan batun dangan taka tsakaninsa da shugaban Barcelona, inda ya ja bakinsa ya yi shiru.

Barcelona na fama da kalubale a bana tun bayan da Lionel Messi ya bar kungiyar ya koma Paris St Germain, inda Benfica ta doke ta 3-0 a tsakiyar mako a gasar Champions Legue.

Kungiyar mai kwantan wasa tana ta shida a teburin La Liga da tazarar maki biyar tsakaninta da Real Madrid ta daya a teburi, wadda za ta fafata nata wasan ranar Lahadi

Related posts

Leave a Comment