Ali Kachalla shi ne jagoran ’yan bindigar da ya kitsa ya kuma jagoranci kakkabo jirin yakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya a Jihar Zamfara.
Duk da cewa ba a san shi sosai ba, bincikenmu ya gano cewa ’yan bindiga akalla 200 ne suke karkashinsa, kuma su ne suka addabi garin Dansadau na Jihar Zamfara a baya-bayan nan, inda suka kona motar yaki.
A ranar 18 ga watan Yuni ne ’yan bindiga suka harbo jirgin yaki, wanda Rundunar Sojin Saman ta ce an bude masa wuta ne a hanyarsa ta dawowa daga yakar ’yan bindiga a iyakar Jihar Zamfara da Jihar Kaduna.
Har yanzu ba a bayyana hoto ko bidiyon jirgin ba, amma mun kawo rahoton yadda matukin jirgin, Flight Lieutenant Abayomi Dairo, ya yi saukar lema, daga bisani ya yi ta sanda har ya shiga wani kauye ya boye, daga baya mutanen kauyen suka taimaka masa ya je wani sansanin sojoji.
Hukumomi ba su bayyana ainihin wanda ke da hannu a harbo jirgin sojin ba, amma bincikenmu ta majiyoyin tsaro da wasu mazauna yankin sun bayyana mana cewa Ali Kachalla da yaransa ne suka harbo jirgin.
Mun gano cewa Ali, wanda ba a fiye jin sunansa a cikin ’yan bindiga ba, yana zaune tare da yaransa ne a cikin Dajin Kuyambana wanda ya ratsa jihohin Zamfara da Kebbi da Kaduna da kuma Neja.
Mazauna a yankin Dansadau a Jihar Zamfara sun dade da sanin shi domin ya addabe su da hare-hare, musamman a baya-bayan nan, kuma yana yawan yi wa sojoji kwanton bauna.
Wane ne Ali Kachalla
Ali matashi ne mai shekara 30 da wani abu haifaffen kauyen Madada ne da ke kusa da garin Dansadau.
Wani wani wanda ya san yankin a ce a halin yanzu Ali Kachalla da yaransa sun yi sansani a gabar Kogin Goron Dutse, wanda ya ratsa tsakanin iyakokin jihohin Kaduna da Zamfara. Kogin na da nisan kilomita 25 daga Dansadau.
“Akwai bukkoki da yawa a sansanin nasa ta bangaren Birnin Gwari, garken shanunsa da yaransa masu dauke da muggan makamai ke kula da su kuma na ta bangaren Jihar Zamfara.
“Yanzu haka akwai yaransa a kauyukan Dandalla da Madada da kuma Gobirawa Kwacha da ke Kudu Maso Yamma da garin Dansadau kuma ’yan bindiga na yin yadda suka ga dama a kauyukan,” inji majiyar da ta bukaci a boye sunanta.
Ana kwatanta Ali Kachalla da yaransa cewa marasa tsaro ne kuma sun sha kai wa jami’an tsaro hari; Ana kuma ganin yaran nasa sun fi na yawancin gungu-gungun ’yan bindiga yawa.
A baya-bayan nan ne Ali Kachalla ya tsananta kai wa garin Dansadau hari saboda zargin mutanen garin sun taimaka wa matukin jirgin yakin da Alin ya so kamawa da ransa. Yana kuma jin haushi cewa mutanen garin sun dakile hanyar kai wa ’yan bidiga kayayyakin bukata.
Rahoton Jaridar Aminiya
