Babban sufeton janar na ?an sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya amince da na?in DCP Tunji Disu a matsayin sabon shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT),
Wannan na nufin shi zai maye gurbin ?an sanda nan Abba Kyari da aka dakatar kan zargin rashawa.
Sanarwar da ke dauke da sa hannun jami’in ya?a labaran rundunar, CP Frank Mba ta ce DCP Disu zai kama aiki gadan-gadan ba tare da ?ata lokaci ba.
Kuma a cewar sanarwar IGP Alkali na saran sabon shugaban ya nuna ?warewa da jagoranci wajen aikawatar da aikinsa da sauke nauyin da aka dora masa.
Sannan ya tabbatarwa ?an kasa cewa wannan sashi na IRT zai ci gaba da aiki tu?uru wajen kare kasa da manufofinta daga ?ata gari.
Kafin na?in DCP Disu wannan mukamin, shi ne tsohon kwamandan kai agajin gaggawa na Rapid Response Squad (RRS) ta jihar Legas. Kuma ya rike mukamin mataimakin kwamshina a sashin ayyuka na rundunar a hedikwatarta ta Abuja.
Sannan ya rike mukamai daban-daban da ayyuka a fanoni da dama na rundunar.
