Wasu ?an Najeriya a shafukan sada zumunta sun nuna ?acin ransu bayan ganin wani bidiyo da ya nuna yadda wasu matan gwamnoni ke taya uwar gidan shugaban ?asa murnar zagayowar ranar haihuwarta a ?asar Dubai.
A ranar 17 ga watan Fabrairu ne Aisha Buhari ta yi bikin cika shekaru 51 a duniya, amma sai yanzu bidiyon ya fito. Babu tabbaci kan lokacin da aka ?auki bidiyon.
Bidiyon ya nuna wasu gungun mata da kafafen ya?a labaran Najeria suka ce matan gwamnoni ne ?auke da wani ?aton akwati da furanni, suna rera wa?ar murnar zagayowar ranar haihuwa ga Aisha Buhari.
Wasu sun bayyana mamakin yadda wa?anda suka halarci bikin suka kashe ku?in jirgi zuwa Dubai.
“Nawa ne daga cikinsu za su yi amfani da ku?in aljihunsu,” kamar yadda wani mai amfani da Twitter ya bayyana.
Wasu kuma na ganin matan gwamnonin sun kama hanya sun tafi biki a daidai lokacin da ?asa ke fuskantar tarin matsaloli.
