Bauchi: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Nemi Gafarar Cin Zarafin Dan Jarida

Kwamishinan Yan’sanda na Jihar Bauchi Sylvester Abiodun Alabi yayi nadamar abunda Jami’an Yan’sanda suka aikata akan dan’jarida a yayin da yake gudanar da aikinsa na daukan rahoton, hakan ya biyo bayan wani zama na mussaman da akayi tsakanin Uwar Kungiyar Yan’jarida ta kasa da ta Jihar a sakatariyar Kungiyar na Jihar Bauchin.

Tunda sanyi safiyar Asabar ne dai Kungiyar Yan’jarida reshen Jihar karkashin Shugaban ta kwamared Umara Sa’idu ta Shirya wani gagarimin zanga-zangar lumana don nuna fushinta akan cin zarafin da Yan’sanda suke yi ma masu dauko rahotanni ko kuma Yan’jarida a dukkan fadin Jihar, inda rahotanni suka yi nuni da cewa hakan ya faru karo na UKu kenan a cikin shekara daya.

Ana cikin wan nan Shirin zanga-zangar me kwatsam sai ga kwamishinan Yan’sanda ya bayyana a sakatariyar, tare da wasu kusoshi a hukumar Yan’sandan, suna ikrarin suma zasu shiga cikin zanga-zangar lumanan, jim kadan Suka shiga zauren tattaumawa, da Uwar kungiya bayan sun kammala, sai yayi.ma.manema labarai bayanin bayan zaman nasu.

Yace, sun bada hakuri tareda nuna alhinin su, Kuma hakan bazai sake faruwa ba, yace kowa na bukatar kuwa kafin yace nasara a wajen gunar da aikinsa, saboda haka nan take yace ya rushe wan nan bangare na Yan’sanda ta Rapid Response Squad (RRS) sainabinnda Hali yayi, a turance.

Kuma yace tuni hukumar ta mayar ma da dan’jaridar Na’urar naukan hoton, da Kuma alkawarin biyan dukkan kudin da aka kashe a asibiti na jinyar shi, tare da biyan dukkan wani kayan aikin dan’jari dan da suka salwanta a sakamakon dukan da yasha a hannun Yan’sandan.

Har ila yau kwamishinan Abiodun Alabi yace zai hada wani horarwan na musamman tsakanin yanjaridar Jihar da Masu kana matsayin na Jami’an Yan’sanda don kowa ya fahimci aikin sa tare da wayarwa da Yan’sanda kai, a harkokin aikin dan’jarida

Bugu da kari, ya roki Kungiyar ta NUJ da su Kanye zanga-zangar lumana da suka Shirya, a cewarsa ana tare komai wahala,

A daya bangaren kuwa Sakataren na Uwar Kungiyar Yan’jarida ta kasa Shu’aibu Usman Leman, ya kara da jan kunne Yan’sanda da su rika martaba Yan’jarida a ayyukansu kana su gane mu abokan aiki ne ba abokan gaba ba.

Kana ya jinjina ma Kwamishinan Yan’sandan da sa baki a cikin lamarin Kuma akan kari domin a Samun dai-daito da zaman lafiya da hadin Kai da Yan-jarida a fadin Jihar Bauchin baki daya.

Duk da haka Kungiyar Yan’jariddan na Jihar tace batun daukan rahoton Yan’sanda babu shi har yanzu sai munga abinda ya chanza a sakamakon zaman da akayi kan wan nan batu

Kana ta kirayi yayan Kungiyar da su kwantar da hankalinsu zasu da Ido a tsakanin dangantakar Yan’sanda da Yan’jarida a Jihar don samar da kyakyawar yanayi a wajen gudanar da aikinsu na dauko rahotanni.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment