Zagin Annabi: Zan Sa Kafar Wando Guda Da Masu Tada Fitina – Gwamna Bala

Daga Adamu Shehu Bauchi

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya kai ziyarar gaggawa a Karamar hukumar Warji inda aka samu tarzoma da barkewar rikici kan tsokacin da wata mai aikin a asibitin a garin ‘yar shekara arbai’n da haihuwa tayi game da batancin da Deborah tayi a Sokoto a kwanan baya da kuma turawa a kafafen sadarwa na zamani, abinda ya harzuka matasan yanki, suka far mata.

Bala yaja kunnen duk wadanda suke da hannun kan rikicin da kuma sake tada husuma mai kama da irin wannan, su kuka da kansu a cewarsa zai sa kafar wando daya dasu da masu goya masu baya.

Zan kama Shugaban karamar hukumar da Hakimi da dan’majalisar jiha da Pasto da Liman na yankin, indai na sake Jin wani abu makamancin haka, domin mu a jihar Bauchi an sanmu da zaman lafiya, kabilu dabam dabam, in Allah yaso sai yayi mu dukkanmu Kiristoci, ko Kuma Musulmi dukkan mu, babu abinda yafi zaman lafiya dadi, Ina ?ara jan kunne kowa ya shiga taitayin sa akan zaman lafiya” Gwamnan ya jaddada.

Kwamishinan Yan’sanda na Jihar Umar Mamman Sanda shima, yayi bayani kan irin matakan da jami’an tsaro Suka dauka tare da gargadi al’ummar yankin Warji da su rungumi zaman lafiya, tare da gujewa dauka doka a hannunsu, musamman matasa da masu tasowa a cikinsu

Kwamishinan yace “babu abinda yafi zaman lafiya dadi, sabo da haka ya zama dole mu tashi tsaye domin kare rayukanku da dukiyoyinku, domin samun cigaba mai inganci ga kowa, yace ba zamu yi kasa a gwiwa ba”

Ita dai wacce ake zargin da yabawa game da batancin da Deborah tayi a jihar Sokoto a kwanan baya, kuma ta tura a group na (social media na asibitin da take aiki a garin Warjin mai suna Rhoda Jatau, kana ta tsallake a lokacin da matasan suka harzuka suka nufi gidan da akace an boyeta, amma basu same ta ba.

Related posts

Leave a Comment