Kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, ta koka kan abinda ta kira rashin adalci da gwamnatin tarayya ke mata musanman a bangaren gine-ginen manyan tituna da sauran muhimman ayyuka a yankin.
?ungiyar wadda ta hada da gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno Gombe, Taraba da Yobe ta bayyana hakan ne a ranar Juma’a cikin sakon bayan taro mai dauke da sa hannun shugabanta ?ungiyar Gwamna Jihar Borno Babagana Zulum a karshen taronta na 3 da aka yi a Yola babban birnin Jihar Adamawa.
Kazalika, kungiyar ta nuna rashin jin dadinta kan tafiyar hawainiya ko rashin samun cigaba’ kan yadda ake gudanar da kwangilolin ayyukan titi da aka bayar a yankunan.
“Kungiyar ta lura cewa ma’aikatan ayyuka da gidaje ta gwamnatin tarayya bata yi wa yankunanta adalci a bangaren gine ginen tituna.
Har wa yau, kungiyar bata jin dadin jan-kafa ko rashin cigaban ayyukan tituna da aka bada a yankunan ta kuma ta yi kira da cewa a cigaba da ayyukan nan take tare da yin bita kan sauran ayyukan tituna da aka bada a yankin.
