Goyon Bayan Ta’addanci: Ya Kamata A Tsige Maqari Daga Limanci – Soyinka

Fitaccen marubucin nan mazaunin ?asar Amurka Farfesa Wole Soyinka, ya yi kira da a sauke limamin babban masallacin kasa na Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, daga mukaminsa kan kalaman da ya furta game da kisar Deborah Yakubu, dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari a Sokoto saboda zagin Annabi (SAW).

Soyinka ya zargi limamin da umurtar mabiyansa su dauki doka a hannunsu da sunan addini, wanda hakan ya ci karo da halayyar shugaba na addini musamman babban Limamin Masallacin ?asa.

Ya yi wannan jawabin ne a ranar Asabar a Abuja yayin taron shekara guda da rasuwar tsohon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da kaddamar da littafin tarihinsa da marubuci Niran Adedokun ya rubuta.

Soyinka ya nuna rashin jin dadinsa game da kisa da sunan addini, ya kara da cewa ‘Ya zama dole a cire wanda ya kauracewa tsarin mutuntaka. “Ba za mu lamunci musulmi su rika fakewa da cewa musulunci ya ce kaza da kaza ba, ko Sharia kaza da kaza ne, ko kuma Annabi Mohammed (SAW) ya yi misali iri kaza ko ya furta magana na jin kai iri kaza ba suna aikata ta’addanci.

Farfesa Soyinka ya ce malamin na addinin musulunci ba komai ya yi ba illa karfafawa mabiyansa gwiwa su kashe duk wani da ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW). Ya cigaba da cewa: “Farfesa Maqari da wasu tsiraru, ciki har da yan sanda a baya-bayan nan ba su nuna nadama ba bisa azabtarwa da kashe dalibar Sokoto”

Maqari a kaikaice ya umurci mabiyansa su dauki doka a hannunsu da sunan addini. Wannan shine sakon malamin addinin ga kasar da ke fuskantar abubuwa na rashin hankali.”

Related posts

Leave a Comment