Mai neman takarar shugabancin kasa a jamiyar APC Rotimi Amaechi yace idan aka zabe shi shugaban kasa zai mai da hankali wurin bunkasa noma don ha?aka masana’antu da za su taimaka wurin bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
Rotimi Amaechi wanda shine tsohon gwamna jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri yace ya bada kwarewar da zai yi amfani da ita wurin kawo ?arin cigaba idan aka zabeshi Shugaban kasa a za?en 2023.
Rotimi Amaechi ya bayyana haka ne yayin ziyarar shi jihar Gombe don tuntuba da kuma yin taro da wakilai wato delegates na Jami iyar APC a jihar ta Gombe.
Ya ?ara da cewa zai yi iya kokarin shi ya gyara hanyar jirgin kasa na Gombe zuwa Maiduguri zuwa Fatakwal, yana mai ?arawa da cewa zai kuma tabbatar da cewa ya tafi da Mata da Matasa don basu damar bada gudunmawarsu na ciyar da Nijeriya gaba.
Da yake magana a wajen taron tsohon gwamnan jihar Adamawa Sanata Jibrila Bindow, wanda yana cikin tawagar Rotimi Amaechin yace Rotimin yana da kwarewar da zai kai Nijeriya zuwa ga tudun mun tsira kuma zai agaza wurin tabbatar da sake gina arewa maso gabas da ‘yan tada kayar baya suka ?ai?aita domin mutum ne wanda zai yi shugabanci ba tare da nuna banbanci ba.
