Zabukan Shugabannin APC Ya Bar Baya Da Kura A Jihohi

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta gudanar da taron gangami na jihohi a ranar Asabar, 16 ga watan Oktoba, inda aka yi zaben shugabannin jam’iyyar na jihohi a fadin Najeriya a jihohi 36.

Sai dai, jihohi da yawa sun ga sabon lamari inda aka samu baraka da rarrabuwar kai a yayin zaben, da darewar shugabanci gida biyu a mafiyawancin Jihohin, yayin da jam’iyya mai mulki ke fafutukar ganin ta gyara gidanta kafin 2023.

A kasa mun kawo jerin jahohin da jam’iyyar APC mai mulki ta samar da shugabanni guda biyu sabanin daya da ya wanda yake bisa ga tsari.

1. Jihar Osun: A Osun, bangarori biyu na APC sun gudanar da taron gangamin don zaben sabon shugaban jam’iyyar.

Bangaren da ke biyayya ga Gwamna Gboyega Oyetola an sake zabar Gboyega Famodun a matsayin shugaba. A gefe guda kuma, bangaren da ke biyayya ga Rauf Aregbesola, tsohon gwamnan jihar kuma ministan harkokin cikin gida, an zabi Rasaq Salinsile a matsayin shugaban APC.

2. Jihar Legas: A Legas, Cornelius Ojelabi ya fito a matsayin shugaban jam’iyyar APC a jihar ta hanyar ittifakin. Sai dai kuma wani bangare mai suna Lagos4Lagos Movement ya zabi Sunday Ajayi a matsayin shugaban APC.

Hakanan a Legas, wani bangare da ake zargin yana biyayya ga tsohon gwamna Akinwumi Ambode ya samar da Beatrice Omotayo Tugbobo a matsayin shugaban APC.

3. Jihar Kwara: A jihar Kwara, bangaren Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu, ya samar da Bashir Bolarinwa a matsayin shugaban APC. A gefe guda kuma, bangaren da ke biyayya ga AbdulRahman AbdulRazaq, gwamnan jihar Kwara, sun zabi Sunday Fagbemi a matsayin shugaba.

4. Jihar Akwa Ibom: A bangaren da ke biyayya ga Godswill Akpabio, ministan harkokin Neja Delta, an zabi Steve Ntukekpo a matsayin shugaban APC. A daya bangaren kuma, Austin Ekanem ya fito a matsayin shugaba a bangaren da Akpan Udoedeghe ke jagoranta, mukaddashin sakataren jam’iyyar APC na kasa.

5. Jihar Kano: A jihar Kano ta dabo kuwa, bangaren da Gwamna Abdullahi Ganduje ya amince da shi ya samar da Abdullahi Abbas a matsayin shugaba, Sai dai bangaren da Malam Ibrahim Shekarau ke jagoranta ya zabi Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban APC a wani taron na gangami na jihar.

6. Jihar Ogun: A jihar Ogun, bangaren masu biyayya ga Gwamna Dapo Abiodun sun zabi Yemi Sanusi a matsayin sabon shugaban jam’iyyar ta APC yayin da bangaren Ibikunle Amosun, tsohon gwamnan jihar, suka zabi Derin Adebiyi a matsayin shugaban APC.

7. Jihar Neja: A jihar Neja, an kuma gudanar da taron gangami a wurare biyu. Haliru Jikantoro ya fito a matsayin shugaban bangaren da Gwamna Abubakar Sani-Bello ya amince da shi yayin da wani bangaren kuma ya zabi Nasiru Ubandiya a matsayin shugaban APC na jihar.

8. Jihar Enugu: Batun bai sauya ba a jihar Enugu. Yayin da wani bangare ya samar da Adolphus Ude a matsayin shugaban APC, wani kuma ya samar da Ugochukwu Agballah.

Related posts

Leave a Comment