Shugaban kungiyar tsagerun Inyamurai ta IPOB dake son kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya nemi mabiyansa su yi yajin vin abinci kamin zuwan ranarbda za’a gabatar dashi a gaban kotu.
Kanu ya nemi hakanne ta bakin lauyansa, Ifeanyi Ejiofor wanda yace yana cikin koshin lafiya.
Yace maganar da ake yayatawa wai an fitar fa Kanu zuwa kasar China ba gaskiya bace.
Yace kuma gwamnati ta kammala bincikenta akan lamarin dan haka babu wani dalili da zai hana gabatar da Kanun ranar 21 ga watan October.
Yace yana kira ga mabiyansa dasu ci gaba da bashi goyon baya da kuma bin doka kamar ya da suka saba.
