Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar wasu tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da dagacin garin Banye, dake ?aramar hukumar Charanchi, jihar Katsina cikin dare.
An ruwaito cewa maharan sun sace dagaci, Alhaji Bishir Gide Banye, tare da wani mutum ?aya da ake tsammanin ?alibin sakandare ne.
Wani mazaunin garin ya tabbatar da cewa maharan ?auke da makamai sun mamaye garin Banye ranar Jumu’a da daddare. A cewar mutumin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, maharan sun tafi kai tsaye zuwa fadar basaraken, inda suka sace shi tare da wani mutum ?aya.
Duk da cewa Banye na ?aramar hukumar Charanchi, amma datse hanyoyin sadarwa da aka yi a ?aramar hukumar Kurfi ya shafe su. Wannan matakin na datse sabis, ya sanya maharan sun ci karensu babu babbaka domin mazauna garin ba zasu iya sanar da jami’an tsaro ba, a kawo ?auki.
Wannan shine karo na biyu da yan bindiga suka sace dagaci a yankin, domin a baya an ta?a sace basaraken Barkiya dake karamar hukumar Kurfi, har sai da aka biya makudan kudade na fansa.
Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda, reshen jihar Katsina, SP Gambo Isah, yace basu samu rahoto a hedkwatar yan sanda ta jiha ba zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.
