Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje ya gargadi makiyaya su guji aikata laifuka ko kuma su fuskanci hukuncin kisa ko daurin rai da rai, ba tare da ?ata jinkiri ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da ya ke kaddamar da shirin yi wa dabobi rigakafi a Kadawa, karamar hukumar Garun Mallam.
Gwamna Ganduje ya ce jiharsa ta tanadi hukuncin kisa ko daurin rai da rai ga makiyaya masu kai hari ko yunkurin tayar da hankulan jama’a.
Ganduje ya ce a maimakon su yi rikici, ya kamata su rungumi tsarin kiwo na zamani su inganta tattalin arzikinsu tare da dogaro da kai, wato su yi tafiya da tsari na zamani.
“Na yi farin cikin ganin muna zaune lafiya a nan ba tare da rikicin makiyaya da manoma ba a Kano. Don haka, ina shawartar ku da ku guji aikata laifi ku rungumi kiwo. Muna da doka a Kano kuma duk wanda aka kama yana satar shanu ko dan bindiga, zai fuskanci daurin rai da rai ko hukuncin kisa.”
A cewar Ganduje, jiharsa na fatan yi wa shanu miliyan daya rigakafi a shekarar 2022 domin inganta kiwo a jihar. Ya ce gwamnatin jihar ta dauki ma’aikata lafiya guda 220 da za su yi aiki tare da makiyayan domin bunkasa kiwonsu da tattalin arziki.
Ya ?ara da cewar nasarar da aka samu a bara ya janyo cigaba sosai a bangaren kiwon don haka akwai bukatar a kara rubanya nasarorin, yana mai cewa kiwo na cikin abubuwan da gwamnatin tarayya ta mayar da hankali a kai.
