Cristiano Ronaldo ya dawo Manchester United bayan shekaru 12 da kafar dama yayinda ya zura kwallaye biyu a nasarar da United ta samu kan Newcastle ranar Asabar.
Manchester United ta lallasa Newcastle 4:1 a filin wasansu ta Old Trafford. Yanzu dai Ronaldo na da jimillar kwallaye 120 a wasar Firimiya.
Ronaldo ya zura kwallon farko ne a minti 45 + 2 ana gab da zuwa hutun rabin lokaci, kafin J. Manquillo na Newcastle ya rama a daidai minti na 56.
Bayan minti 8 da Newcastle ta rama, Ronaldo ya sake zura kwallonsa ta biyu a minti na 62.
Manchester ta fara shakar kamshin nasara kenan Bruno Fernandes ya ci wata kwallo maikyau daga nesa a minti na 80. Yayinda ake gab da shi a minti na 92, Jesse Lingard, ya zura kwallo ta hudu bayan tsawon lokaci bai takawa Manchester leda ba.
