Tozarta Sarki: Masarautar Kano Ta Ba Kamfanin Air Peace Wa’adin Neman Gafara

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Kano na bayyana cewar Shugaban tsare-tsare na masarautar Isah Bayero, ya ba Kamfanin Jiragen sama na Air Peace sa’o’i 72 su bai wa mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, hakuri bisa wulakantashi da suka yi da jinkirta tafiyarsa.

Malam Isah Bayero ya bayyana hakan ranar Asabar yayin hira da wasu manema labarai a jihar Kano, kan takkadamar da ta faru tsakanin Sarki da Kamfanin Jiragen saman.

Ya ?ara da cewar wajibi ne kamfanin Air Peace ya amsa cewa yayi laifi wajen kin bin tsari, wanda haka ya sabbaba jinkirin Sarkin Kano a tashar jirgin Legas.

“Tunda mun yi jinkirin barin Banjul da awa guda, ya kamata su sani da akwai fasinjoji goma dake niyyar zuwa Kano kuma suyi abinda ya kamata saboda ba laifinmu bane jinkirin da ya faru.”

“Na kirasu sau da dama amma suka ki daukan waya sai daga baya sukace ba zai yiwu ba.Ya kamata shugabannin kamfanin su rika yiwa manyan mutane shiri na musamman.” “Tun da sun jinkirta tashinmu daga Banjul, wanda ya sabbaba jinkirin zuwa Legas, ya kamata Air Peace ya shirya yadda za’a yi.

Amma babu abinda sukayi.” “Ina basu sa’o’i 72 su bai wa Sarki hakuri, na farko a jarida, na biyu kuma su turo wakilai wajen Sarki. Babu abinda ba zamu iya yi don kare mutunci masarautarmu ba.”

Related posts

Leave a Comment