Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar za?e ta ?asa INEC ta sanar da jadawalin babban za?e na 2023, inda za a gudanar da za?en shugaban ?asa ranar Asabar 25 ga watan Fabarairun 2023.
Shugaban INEC Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Asabar.
Kazalika, za a gudanar da za?en ‘yan majalisun tarayya tare da na shugaban ?asar.
Za?en gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi zai gudana ranar 11 ga watan Maris na 2023 ?in.
A cewarsa, an za?i ranar ce saboda a tabbatar an yi aiki da sabuwar dokar za?e, wadda ta tanadi cewa wajibi ne a bayyana ranar za?en a?alla kwana 360 kafin ka?a ?uri’a.
Ya ?ara da cewa hukumar za ta wallafa sauran tanade-tanaden dokar za?en “a lokacin da ya dace”.
