Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a ranakun Lahadi da Litinin za a sauko da tutoci a fadin kasar, da kuma a ofisoshin jakadancin kasashen waje domin nuna girmamawa ga Sarauniyar Ingila Elizabeth II wacce ta rasu a ranar Alhamis.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin kasashen wajen kasar ta fitar, ta ce Sarauniyar ta ”Nuna kwazo a tsawon lokacin da ta shafe a kan karagar mulkin Birtaniya, kuma shugabar Kungiyar Kasashe Rainon Ingila”
”Haka kuma ta nuna jajircewa wajen wanzuwar zaman lafiya da hadin kai tsakanin kasashe” in ji sanarwar.
Tuni dai gwamnatin Najeriya ta mika sakon ta’aziyyarta tana mai cewa Birtaniya da Najeriya sun kasance cikin kyakkyawar dangantaka karkashin mulkin Sarauniyar.
Najeriya ce dai kasa mafi girma a Afirka da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka.
