Magudin Zabe Ya Zo Karshe A Najeriya – INEC

Shugaban Hukumar Za?e ta ?asa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa sabbin dabarun killace al?aluman za?e ta hanyar na’urori da manhaja sun tabbatar da cewa zamanin baddala sakamakon za?e ko yin kutse cikin rumbun tattara bayanai ya wuce.

Yakubu ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin za?e da YIAGA Africa ta shirya a Abuja.

Ya ce ko a za?en gwamnan Jihar Ekiti da na Osun da aka yi baya-bayan nan, ‘yan kutse da ?asashe daban-daban har da wasu daga nahiyar Asiya, sun yi ?o?arin kutsawa rumbun tattara bayanan INEC ta cikin manhaja domin su baddala al?aluman za?e, amma ba su yi nasara ba.

Daga nan ya ?ara jan kunnen ma’aikatan hukumar da masu sa-ido cewa tilas sai an ?ara sa ido sosai kuma an ?ara ?arfafa hanyoyin hana ‘yan kutse shiga manhajoji domin baddala sakamakon za?e.

Related posts

Leave a Comment