2023: Tinubu Ne Mafi Cancantar Zama Shugaban Kasa – Abu Ibrahim

An bayyana ?an takarar shugabancin ?asa a ?ar?ashin jam’iya mai mulki ta APC Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda ya fi sauran ‘yan takara cancanta da zama shugaban ?asa a babban za?e dake tafe na shekarar 2023.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin jigo a jam’iyyar APC tsohon Sanata daga Jihar Katsina Sanata Abu Ibrahim, a yayin tattauna da aka yi dashi a cikin Shirin Ina Dalili na gidan Talabijin na Liberty dake Abuja.

Sanata Abu Ibrahim ya cigaba da cewar samun nasarar da Tinubu ya yi a za?en fidda gwani da aka yi na jam’iyyar ya biyo baya ?wazo da yake dashi da kuma tarin nasarorin da ya samu a zama gwamna da yayi na shekara 8 a Jihar Legas.

Dangane da korafin da wasu ke yi na cewar takarar Tinubu da Shettima za ta haifar da matsala a kasa ta la’akari da cewa dukkanin su su biyun Musulmai ne Sanata Abu Ibrahim ya ce ko ka?an ba haka bane.

“Siyasa lissafi ce kuma da lissafi aka yi amfani wajen za?ar su domin ita ce hanya mai ?ullewa da za ta kai jam’iyyar APC ga samun nasara”.

Jigon Siyasar ya tabbatar da cewa APC za ta yi nasara a za?en dake tafe da tarin ?uri’un ‘yan Najeriya kuma tabbas Tinubu zai kai kasar ga tudun mun tsira.

Related posts

Leave a Comment