Za A Kawo Karshen Matsalar Lantarki Ba Da Jimawa Ba – Gwamnatin Tarayya

Rahotanni dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta ce an samu matsala ne a babban layin samar da lantarki na ?asa, lamarin da ya haifar da rashin wuta.

Wata sanarwar daga ofishin ministan lantarki Injiniya Abubakar Aliyu ta ce ana gudanar da bincike domin gaggauta magance matsalar da ke ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya.

Rahotanni sun bayyana cewar an fuskanci katsewar lantarki a sassan daban daban a fa?in Najeriya ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce: “muna sanar da al’umma cewa matsalar ta faru ne karfe 06:30 a ranar 8 ga Afrilu, wanda ya haifar da matsalar lantarki a sassa da dama na ?asa.”

Kungiyoyi daban-daban a Najeriya na cigaba da nuna dawuwa da takaici na matsalar yankewar lantarki da rayuwa cikin duhu da jama’a ke yi a Najeriya.

Related posts

Leave a Comment