Rahotanni daga birnin Tehran na kasar Iran bayyana cewar kasar na shirin gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa da abokiyar hamayyarta Saudiyya a Ira?i bayan kafa sabuwar gwamnatin Iran, kamar yadda aka ambato jakadan Iran a Bagadaza yana cewa a ranar Talata
Iran da Saudiyya wa?anda su ne jagororin Shi’a da Sunni a Gabas Ta Tsakiya sun shafe shekaru suna hamayya da juna inda dukkaninsu ke marawa ?angarori da ke ya?i a Yemen da Syria da wasu wuraren.
A 2016 suka katse hul?ar diflomasiya tsakaninsu.
A watan Mayu Iran ta fara tabbatar da cewa tana tattaunawa da Saudiyya, tana mai cewa za ta yi ?o?arin sun sansanta tsakaninsu.
Tun lokacin ne Iran ta za?i mai tsattsauran ra’ayi Ebrahim Raisi, matsayin shugaban ?asa wanda aka rantsar a ranar 5 ga Agusta.
Sanarwar sabuwar tattaunawar da kamfanin dillacin labarai na ISNA ya sanar na zuwa ne bayan taron ?asashen yankin da aka gudanar a Badadaza kan tsaro.
