Buhari Ya Sa Hannu A Dokar Tsawaita Ritaya Ga Malamai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu kan dokar da ta ?ara wa’adin ritayar aiki ga malaman makaranta mai suna Harmonised Retirement Age for Teachers in Nigeria Act, 2022.

Mai magana da yawun Fadar Shugaban ?asa Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.

An ?ir?iri ?udirin dokar don a samar da tsari a hukumance da zai mayar da shekarun ritaya zuwa 65 maimakon 60 ga malaman makaranta sannan ya tsawaita shekarun aiki daga 35 zuwa 40, a cewar Ministan Ilimi Adamu Adamu.

Related posts

Leave a Comment