2023: Mace Zan Dauka Mataimakiya Idan Na Zama Shugaban Kasa – Yahaya Bello

Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce zai ?auki mace ta yi masa mataimakiya idan jam’iyar APC ta tsaida shi takarar shugaban ?asa a 2023.

Bello ya baiyana hakan ne a wani taron karawa juna sani da ?an jarida masu rahoton labaran siyasa da na kotu a jiya Juma’a a Abuja.

A cewar Bello, zai baiwa mata muhimmanci idan har a ka bashi dama ya za?i wanda zai yi takara da shi.

Gwamnan ya ce ya na da burin yin gwamnati da za ta tafi da kowa, musamman mata, matasa da masu bu?ata ta musamman.

Ya ?ara da cewa haka ya ke gudanar da mulkinsa a Kogi in da bai bar kowa ba wajen tafiyar da gwamnatinsa.

Bello ya ?ara da cewa idan ya samu dama, zai samar da tallafi ga matasa da mata domin bun?asa tattalin arziki.

Related posts

Leave a Comment