Za a buga wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai watau Champions League na bana a Paris, bayan da aka dauke daga Rasha saboda kutsen da kasar ta yi a Ukraine.
A baya an shirya buga wasan mafi girma a Turai a filin wasa na Gazprom Arena da ke St Petersburg a ranar 28 ga watan Mayu.
Amma a yanzu hukumar kwallon Turai – UEFA ta ce a filin wasa na Stade de France da ke Paris.
Hukumar Uefa ta nuna godiya ga shugaban Faransa, Emmanuel Macron saboda “nuna goyon baya da taimakon da yake bai wa kwallon kafa a Turai.”
