?ungiyar ASUU ta mayar da martani kan kalaman na Buhari, Inda ta ce ta yi mamakin kalaman na shugaban.
Farfesa Abdulkadir Muhammad shugaban ASUU shiyyar Kano ya shaida wa BBC cewa ba su ji da?in kalaman na Buhari ba, yana mai cewa “maganar ta fito ne daga bakin mutumin da kamar bai san abin da ke faruwa ba ko halin da kasa ke ciki.”
“A tunaninmu a matsayinsa na shugaban kasa, wannan yajin aikin ba yau muka fara ba, yau an shiga wata biyar, sai muke ganin ?ila ya farka daga bacci ne. Ko kuma ya da?e bai yi magana ba yanzu ne ya ga damar yin magana kan yajin aikin.”
“Mun yi watanni ba albashi, kuma hakan bai sa mun mutu ba. Don haka maganar fatar baki ba za ta yi maganin yajin aikin ba sai idan gwamnati ta yi abin da ya kamata,” in ji shi.
Ya ?ara da cewa idan har Buhari ya ce yajin aikin ya isa haka nan, to ai shi ne ya kamata ya ?auki matakin ganin an kawo ?arshensa.
ASUU ta ce kwamitin da shugaban ya kafa ne ya kamata ya kira ya fada masu cewa zaman ya isa hakan nan kuma yana son sanin dalilin da ya sa ba a janye yajin aikin ba.
“Komi yana hannun gwamnati idan ta ga dama a janye za a janye,”
Maganar da Buhari ya yi ya nuna wa ?an Najeriya cewa gwamnatinsa ta gaza ko ba ta san me take yi ba kan muhimmancin ilimi,”
