Shugaban rukunin Kamfanin Atar communication, mamallakan Gidajen Rediyo da Talabijin na Liberty, Dr Ahmed Tijjani Ramalan ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan sanya hannu a sabon kudirin Dokar Zabe da ya sanyawa hannu a jiya 25 ga watan fabarairu.
Dr Ramalan wanda daya ne daga cikin jiga jigan jam’iyyar APC a kasa ya taka muhimmiyar rawa wurin yada manufofin shugaba Buhari a zaben 2015 da 2019.
Shugaba Buhari yayi abinda ya dace a lokacin da ya dace, sannan tarihi ba zai taba mantawa da bunkasa mulkin dimokaradiyya a Nigeria da yankin Africa.’ inji Ramalan’
Ramalan ya kara jinjinawa Yan majalisa kan aikin da sukayi ba dare ba rana wurin ganin an samu nasarar da aka samu na sabuwar Dokar zaben. Sabon tsarin da shugaba Buhari ya sanyawa hannu zai kawo cigaba sosai a harkar zaben kasar mu najeriya.
Daga karshe, Dr Ramalan ya shawarci yan najeriya musamman yan jihar kaduna dasu tashi tsaye wurin yin katin zabe da akeyi yanzu ta hanya mai sauki Wanda xaka iya yi ta wayarka akan adireshinsu ?
https://cvr.inecnigeria.org
INEC Continuous Voters Registration Portal
Kuma cikin sauki zaka iya samun sabo ko sabunta katin zabenka domin Saida katin zabene zaka iya kawo sauyi musamman a sabon dokar da shugaba Buhari ya sanyawa hannu.
