Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karyata rahotannin cewa an tayar da tarzoma a wajen taron kamfen na jam’iyyar APC a Gashua, karamar hukumar Bade ta jihar Yobe.
Mai magana da yawun Ahmad Lawan, Ola Awoniyi ya fitar da jawabi ranar Lahadi a Abuja, ya bayyana cewa karerayi kawai yan jarida suka yada cewa an yiwa gwamna Mai Mala Buni jifar shaidan.
“Mun samu labarin karya kagaggu a kafafen yada labarai game da taron kamfen APC da akayi a Gashua, karamar hukumar Bade ta jihar Yobe, ranar Asabar, 11 ga Febrairu, 2023.”
“Rahotannin na cewa an tayar da tarzoma a taron kuma mabiyan wani dan siyasa ne suka kai harin, wanda ya kai an yiwa wasu jagororin jam’iyyar rajamu.” “Muna masu bayyana cewa wannan ba gaskiya bane.”
