An bayyana cewar Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba tada kan gado gwamnati ce mai tafiyar kura ba tare da sanin inda tasa gaba ba.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar PDP ta jihar Kaduna Alhaji Aminu Adam a yayin wata ganawa da manema labarai da ya yi a Kaduna.
?an siyasar ya bayyana cewar halin kwan gaba kwan baya da gwamnatin jihar ke yi musamman akan abin da ya shafi harkar karin farashin mai ya nuna ?arara na rashin sanin inda gwamnatin ta sa gaba.
Aminu Adam ya ?ara da cewa an samu cin karo da juna akan batun ?arin farashin Mai daga ?angarori har uku, kwamitin da Gwamnan Jihar Kaduna El Rufa’i ya jagoranta ya fadi magana daban sannan ?angaren da mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya jagoranta shima ya fadi kalma daban yayin da bangaren shugaban kasa ya fadi abu daban ta bakin shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan.
“Matsayin Buhari na babban ministan mai kuma aka samu wannan tanakuli to ya nuna a fili gwamnatin bata san inda ta sa gaba ba a yayin da ta jefe miliyoyin ‘yan Najeriya cikin kangin Talauci”.
Aminu Adam wanda tuni ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar ?an majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar maza?ar Kawo, yace El Rufa’i ya gaza wajen sauke nauyin jama’a dake kanshi ta hanyar musguna musu sannan majalisa ta zama ‘yar amshin shata inda ya sha alwashin samar da wakilci nagari inda ya kai ga nasara.
