Kin Amsar Tsoffin Kudi: Ganduje Ya Kulle Babban Kantin Hada-hada

Gwamnatin jihar Kano ta hannun Hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki da masu siyarwa ta rufe shahararriyar kantin nan mai suna Wellcare, kan kin karbar tsoffin takardun naira a ranar Lahadi, 12 ga watan Fabrairu.

A cewar mukaddashin shugaban hukumar, Baffa Babba Danagundi, an rufe kantin ne jim kadan bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umurnin rufe shi sakamakon ?in amsar tsoffin ku?i.

Ya ce umurnin rufe kantin ya biyo bayan matakin da kantin Wellcare ya dauka na kin karbar tsoffin takardun Naira daga wajen kwastamomi wanda hakan ya sa?a umurnin da gwamnatin jihar ta bayar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Danagundi ya yi gargadi ga sauran yan kasuwa a Kano da su kwana da sanin cewa gwamnatin jihar bata haramta amfani da tsoffin Naira ba, don haka, duk shagon da aka kama yana kin karbar tsoffin kudin zai fuskanci mummunan hukunci.

Kantin da aka rufe ya nemi afuwa a wajen gwamnati Jim kadan bayan rufe kantin ‘Wellcare Alliance Limited’ ya rubuta wasikar ban hakuri zuwa ga gwamnatin inda ya nemi a gaggauta shiga tsakani don sake bude kantin.

Related posts

Leave a Comment