Buhari Na Zagaye Da Miyagun Fadawa – El-Rufa’i

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna cibiyar Jihohin Arewa na bayyana cewar Gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai, ya sake sakin kalamai masu zafi yayin da ake shirye-shiryen tunkarar babban zabe a watan da muke ciki.

A ‘yan kwanakin nan El-Rufa’i ya haddasa kace-nace musamman kalamansa kan tsarin sauya fasalin naira da CBN ya tsiro da shi da sukar ?ungiyar Dattawan Arewa.

Gwamnan ya namaye kanun labarai musamman lokacin da ya ce akwai wasu, “‘yan kanzagi a fadar shugaban kasa,” da ke yakar ?an takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu.

A wata hira da ya yi da jaridar Premium times Gwamnan El-Rufa’i ya ce a yanzu ya daina aminta da nagartar jagorancin mutanen da ke kewaye da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

“Na aminta da Buhari, kuma har yau na yarda da shi ba zan daina ba amma wa?anda ke kewaye da shi na daina amanna da su, bana aminta da matakin da suka ?auka ko wani aiki da ya fito daga gare su.”

Idan baku manta ba a cikin shirin Channels tv a farkon watan nan, Gwamnan ya ce wasu mutane sun shiga rigar Buhari suna kokarin cimma wata manufa saboda wanda suka so ya sha kaye a zaben fidda gwanin APC.

“Na yi imani cewa akwai wasu mutane a fadar shugaban kasa da suke fatan mu fa?i za?e saboda ba su samu abinda suke so ba. Suna da nasu ?an takara amma bai yi nasara a zaben fidda gwani ba.” “Suna ta kulla-kullan yadda zasu ga mun sha kaye a za?e kuma suna nan sun ?uya a bayan shugaban kasa suna angiza shi ya yi abinda yake ganin ya dace.”

Related posts

Leave a Comment