Rahotannin dake shigo mana daga Makurdi babban birnin Jihar Binuwai na bayyana cewar kawo yanzu sojoji biyu da fararen hula 15 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da yan bindiga suka kai kan garuruwa uku a karamar hukumar Apa ta jihar.
Mazauna yankin sun bayyana cewa an kai hare-haren ne a lokaci guda da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Talata, a garuruwan Opaha, Odogbo da Edikwu a karamar hukumar Apa.
Wani mazaunin yankin da aka ambata mai suna Kole, ya ce gawarwakin mutum 17 ciki harda sojoji biyu ne aka gano daga wasu jeji da ke kusa a safiyar ranar Laraba bayan jami’an tsaro sun kakkabe yankin.
Ya kuma bayyana cewa daya daga cikin sojojin da suka mutu ya kasance kwamandan sashin da ya yi gaba da gaba da maharan ne a kokarinsu na dakile harin.
Shugaban kungiyar ci gaban Apa, Baris Eche Akpoko ya tabbatar da cewar an kai wani hari kan garin a daren ranar Talata, Akpoko ya ce gawarwakin mutane 10 ciki harda na sojoji biyu aka gano amma har zuwa karfe 10:30 na safe bai samu karin bayani kan lamarin ba.
Kwamishinan kudi na jihar, David Olofu, wanda ya fito daga yankin Opaha,daya daga cikin kauyukan da abun ya shafa, ya fada ma manema labarai a Makurdi cewa gawarwaki mazauna kauyen 15 da sojoji biyu aka gano a safiyar Laraba. Olofu ya ce yana hanyarsa ta zuwa kauyen don duba lamarin a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
A halin da ake ciki, kakakin rundunar yan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene, ta sanar wa manema labarai cewa har yanzu bata da masaniya kan lamarin.
